Yadda aka yi muzaharar Ashura a Bauchi

‘Yan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky sun raya ranar Ashura da muzaharar Ashura.

A Da’irar Bauchi, an gabatar a garin Bauchi, Nigeria.

Da misalin karfe 9:00ns almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky na Da’irar Bauchi suka gabatar da muzaharan Juyayin Ashura a yau 10 ga Muharram 1447 (7/7/25) a cikin garin Bauchi.

Sheikh Ahmad Yashi ya jagoranci wannan Muzaharan yayin da masu muzaharar na sanye da bakaken Kaya, tutocin da alami daban-daban na juyayin zaluncin Al’ummah, musamman Al’ummar Gaza da mutanen Palestine.

Haka nan masu muzaharar na raira baitocin juyayin Ashura daban-daban, haka nan ‘Yan tamsiliya na nuna waki’ar Ashura, ana janye da Ahlul Manzo (S) da aka ci mutuncin su a waki’ar Karbala.

Da yawan Al’ummar Musulmi su ma suna jajanta wannan ta’addanci, wanda suke tausayawa abin da ya faru, suna tir da wannan zalunci.

Sheikh Ahmad Yashi a cikin jawabin karkare muzaharar Juyayin Ashura ya dan yi tsokaci a kan abin da ya wakana a waki’ar Ashura. Kuma, ya jawo hankali ga abubuwan da ake amfana daga waki’ar Ashura da ya kunshi:

  1. Raya abubuwan da suka faru a waki’ar Ashura
  2. A bangaren azzalumai aukar da waki’ar Ashura mu yi bahasin abubuwan da suka faru, muna masu la’antar wadanda suka aiwatar da waki’ar, sannan muna masu jimamin wadanda waki’ar ta riske su.
  3. Ya zama muna masu daukar darussan waki’ar Ashura,

Gabatar da wannan bahasin da ya faru na nuna cigaba da daukaka ga wadanda ake zalunta. Kadan daga abin da muke da misalin sa a yau shi ne yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tsaya kyam tana mai kunyata gamayyar azzalumai da ya hada da Israila da kawayen ta. Wannan dai shi ne tafarkin tsira.

Malamin ya kara karfafa tsayuwa a wannan tafarki bisa jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky.

Sheikh Ahmad Yashi, ya kammala muzaharan Juyayin Ashura da aka kammala lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *