Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan.

Sunan Zamfara ya fito ne a lokacin wani taron karramawa na Hukumar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko PHC, wanda ya gudana a katafaren ɗakin taro na ‘Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre’ da ke Abuja a jiya Juma’a.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa a shekarar 2022 ne ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta ƙaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko domin samar da ingantacciyar lafiya a yankunan.

Sanarwar ta Sulaiman ta ƙara da cewa, asusun cibiyar ya mayar da hankali ne wajen ingantawa tare da samar da isassun kuɗaɗe don ƙarfafa wa jihohi 36 wajen samar da kula da lafiya a matakin farko mai aminci da inganci.

Sanarwar ta ce, “Jihar Zamfara ta sami kyautar Dalar Amurka 500,000 a matsayin wacce ta zama zakara a yankin Arewa maso Yamma wajen kula da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko.

“Wannan karramawa da aka miƙa wa Gwamna Dauda Lawal, tallafi ne na haɗin gwiwa tsakanin ‘Bill and Melinda Gates Foundation, United Nations International Children’s Emergency Fund (UNICEF), Dangote Foundation da National Primary Healthcare Development Agency (NPHCDA).’

“Wannan karramawa, ta nuna a fili cewa ayyana dokar ta-baci da Gwamna Lawal ya yi wa fannin kula da lafiya, abin yana haifar da makamako mai kyau da aka tsammata.

“Zamfara da sauran jihohin da suka yi zarra a wannan fanni daga yankunan Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, duk sum raba kuɗi Dalar Amurka Miliyan 6.1 a karo na uku na wannan karramawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *