Tare Ɗanjuma Katsina

An buga wannan rubutun a jaridar ALMIZAN ta ranar Juma’a 17/01/2016. Shekaru 10 da suka wuce.
Tashin hankalin da ya faru a Zariya a watan Disamba da ta gabata ya zama wani lamari da za a ci gaba da tattaunawa a kai har zuwa ƙarshen zamani. Kullum sabbin bayanai suna ta fitowa na abin da ya faru: me ya faru? Ta yaya ya faru? Waɗanne ne suka haifar kuma suka aiwatar da shi?
Wannan lamari ba zai taɓa gogewa ba, domin ya shafi rasa rayukan waɗanda ba su ji ba su gani ba, kuma dangi da zuriyar waɗanda abin ya shafa suna nan da rai. Haka kuma ’yan’uwansu na addini da aƙida suna ji suna gani, suna kuma saurare.
Kamar yadda na faɗa a wani rubutun da na yi a wannan shafin mai taken “Me Ya Kamata Mu Yi?” inda na kawo muhimmancin tattara bayanai da taskace su a irin wannan yanayi, na yi balaguro zuwa Zariya domin ganin inda abubuwan suka faru.
Na ziyarci unguwar Gyallesu inda na tattauna da mazauna yankin kan abin da suka gani, abin da suka ji, da kuma tsokacinsu. Ba wanda na ji daga cikin ’yan’uwa na Harkar Islamiya, domin ma a lokacin da na je, ba kowa ke iya fitowa ya ce shi ɗan’uwa ne ba. In ya yi, matakai biyu ne zai fuskanta; ko dai a zarge shi da leƙen asiri -masu goyon bayan sojoji su yi masa illa don ɓoye abin da suka aikata- ko kuma a ɗauka ya zo ɗaukar fansa ne.
Mutanen Gyallesu sun shaida cewa ’yan’uwa sun nuna jarumtaka irin ta littafan tarihi, jaruntakar da za ta shiga tarihin da za a riƙa karantawa.
Sojoji sun dira Gyallesu tun dare, kuma suka fara aikinsu kamar yadda ganau suka tabbatar.
Sun zo da makaman yaƙi, da shirin yaƙi, da ƙwarin gwiwar cewa cikin mintuna za su kammala, amma mintuna suka koma awanni har rana tsaka, har alfijiri.
A ɓangaren ’yan’uwa kuwa, babu makaman duniya tare da su, sai ƙarfin ikhlasi, ƙarfin zuciya, da imani. Duk da yawan sojoji da makamansu da ƙwarewa, ba su iya shiga gidan Malam (H) ba har cikin dare.
Mutanen Gyallesu sun ce an yi awanni fiye da 10 ba tare da tsayawar harbi ba. Tun daga asuba suka gane cewa ’yan’uwa sun dage, sun hana soja matsowa. Duk wanda aka ji ya jikkata, akwai inda ake kai shi; wanda ya rasu kuwa, akwai inda ake ajiyewa.
Wannan tsayin daka ya tayar wa da sojojin hankali. Sun fara tambaya; idan waɗannan da suke cikin Gyallesu suna irin wannan turjiya ba tare da makami ba, yaya da su waɗanda suke shigowa daga waje?
Saboda haka, sojoji suka toshe duk wata hanya ta shiga Zariya. Suka riƙa binciken duk mota da ke shigowa, suna sauke waɗanda suka yi kama da ’yan’uwa ko kuma ake zaton sun nufo Zariya don kare Malam (H).
Wasu sojoji ma sun bayyana cewa turjiya da jaruntakar ’yan’uwa ta firgita su. Wani soja ya ce ya yi yaƙi da Boko Haram da ma Somaliya da Mali, bai ga irin wannan jarumta ba. Ya ce, “Ko Boko Haram suna gudu idan suka ji mun iso, amma waɗannan ba su gudu.”
Mutanen Gyallesu sun ce sojoji ba su fara samun nasara ba sai abubuwa biyu suka faru:
Na farko: Wasu daga cikin mutanen unguwa suka fara mara wa sojoji baya, suna nuna wa sojoji waɗanda ake zargi. Wasu kuma suna yi musu kirari da goyon baya, wanda sai ya ƙara musu ƙarfin gwiwa.
Na biyu: Yaɗuwar jita-jitar cewa Malam (H) ya bar gida. Wannan ya karya lagon ’yan’uwa, domin tsayuwarsu gaba ɗaya kariya ce ta Malam (H). Da jita-jitar ta yaɗu, sai zuciya ta fara lafawa, wasu ma mata suka cire hijabi suna yafa gyale don kada a gane su.
Sojoji kuma suka ƙara yaɗawa da lasifika cewa sun kama Malam (H), domin su raunana ’yan’uwa. Wasu ’yan unguwa suna yi wa sojoji kirari. Duk da haka, sojoji sun hana ɗaukar hotuna.
Mutanen Gyallesu sun ce sun ga yadda ake fesa wani abu mai kama da iska wanda ke tada wutar da ta ƙone gidan Malam (H), kuma ana jin kukan mutane daga ciki.
Wata tsari kuma, sojoji suka riƙa bari wasu su tsallaka domin yin “ganima”, wanda ya sa wasu daga cikin mutanen unguwa suka shiga cikin wannan tsari suna ɗaukar hotuna suna yaɗawa a social media.
Akwai darussa masu yawa a tsayuwar Gyallesu. Wasu sun rasa ransu, wasu sun jikkata, wasu sun rasa wani ɓangare na jikinsu ko ’yan’uwansu, wasu kuma abokai. Tambaya ita ce: Wane darasi muka ɗauka?
Babban abin koyo shi ne cewa ’yan’uwa sun rasa ransu ne saboda tsayuwa kan gaskiya da kare martabar Malam (H).
Malam (H) ya tsaya a wajen bai motsa ba ne duk da ya rasa ’ya’yansa, ya yi fatan shahada tare da sauran ’yan’uwa ne.

To, kai ɗan’uwa, wane darasi ka ɗauka daga wannan?
Darussa sun haɗa da:
-Addu’a
-Tsayuwa
-Dakewa
-Jajircewa
-Sadaukarwa
-Tsari da shiri
Waɗannan sune ginshiƙai da za su amfani mutum ko’ina yake, idan ya sarrafa su yadda ya kamata.
