Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar sauyi da kuma shaida cewa Zamfara na kan hanyarta ta tashi tsaye da ƙarfi.
An gabatar da kasafin ne a ranar Alhamis a birnin Gusau.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa kasafin kuɗin ya ware Naira Biliyan 714, wato kashi 83 cikin 100, domin ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware Naira Biliyan 147.279 domin ayyukan yau da kullum na gwamnati, wanda ya kai kashi 17 cikin 100.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an tanadi Naira Biliyan 65 domin ilimi, Naira Biliyan 87 domin kiwon lafiyar al’umma, Naira Biliyan 86 a bangaren noma, Naira Biliyan 45 domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya, Naira Biliyan 22 domin kare muhalli, sai Naira Biliyan 17 domin jin daɗin al’umma da tallafa musu.
A jawabinsa gaban majalisar, Gwamna Lawal ya ce gwamnatinsa, wadda aka zaba bisa alƙawarin ceto, gyara da farfaɗo da jihar, ta yi aiki tuƙuru wajen dawo da amincewa ga hukumomin gwamnati, gina manyan sassa, da shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce, mutanen Zamfara da a baya suka shiga damuwa sakamakon sakaci, yanzu sun fara ganin hasken gaskiya, ci gaba da sabon alƙibla.
Ya bayyana kasafin 2026 a matsayin sabon babi a wannan tafiya ta sauyi, yana mai cewa ba tsari ne na kuɗi kawai ba, illa allawari ne na siyasa da nufin tabbatar da zaman lafiya da kuma hanzarta bunƙasar da al’umma ke muradi.
A cewarsa, kasafin an tsara shi ne domin samun ribar tsare-tsaren shirin ceto na matakai shida da gwamnatinsa ke aiwatarwa, waɗanda suka haɗa da ƙarfafa tsaro, sabunta noma domin samar da wadatar abinci, inganta tsarin kiwon lafiya a kowane yanki, faɗaɗa damar samun nagartaccen ilimi, hanzarta raya ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafa matasa, mata da masu rauni.
Gwamnan ya jaddada cewa kashi 17 na kuɗaɗen da aka ware domin kashe-kashen yau da kullum na nuna tsauraran matakan kula da kuɗi da kuma nagartar tafiyar da al’amuran gwamnati.
Ya ce, a ma’aunin ƙasa da kasa, ana ba da shawarar kada irin wannan kashe-kashe ya haura kashi 60, alhali Zamfara ta tsaya nesa da hakan, lamarin da ke nuna kyakyawan yanayin tafiyar da kuɗaɗe bisa ƙa’ida.
Ya kuma bayyana cewa, ginshiƙin kasafin shi ne ɓangaren ayyukan raya kasa da aka ware kashi 83, wanda ya kira tarihi, domin gina manyan ayyuka, karfafa tsaro, farfaɗo da noma, da kuma samar wa matasa damarmaki.
Gwamna Lawal ya ce, babu wani buri da za a cimma, daga tsaro zuwa ilimi, daga noma zuwa gine-gine, daga gyaran ma’aikata zuwa farfaɗo da tattalin arziki, face da cikakken goyon bayan siyasa, jajircewar gwamnati, da haɗa kai da majalisar dokoki.
A ƙarshe, ya miƙa kasafin kuɗi mai taken “Kasafin Tabbataccen Zaman Lafiya da Ci Gaba” na Naira biliyan 861.337 domin nazari da amincewa, yana mai cewa wannan kasafi yarjejeniya ce da al’umma, taswirar sauyi da kuma sanarwar cewa Zamfara za ta tashi tsaye da ƙarfi fiye da da.
