Gwamna Lawal Ya Gana da Majalisar Malamai ta Zamfara, Ya Nemi A Ƙara Addu’o’in Neman Zaman Lafiya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya roƙi Majalisar Malamai ta Jihar da ta ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da dawwamammen tsaro a faɗin jihar.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Majalisar Malamai ƙarƙashin jagorancin Sheikh Umar Kanoma a gidan gwamnati da ke Gusau.

Ganawar ta tattauna kan matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban jihar da sabbin dabarun da za su ƙara inganta wa’azi da karantarwa, tare da mayar da hankali kan yadda irin waɗannan ƙoƙari za su iya gyara tunanin al’umma domin goyon bayan ci gaban Zamfara.

A jawabin sa, Gwamna Lawal ya jaddada muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

Ya ce, “Malamai suna taka muhimmiyar rawa a duk abin da muke yi a Zamfara, domin suna kusa da jama’a, kuma al’umma na sauraron su, musamman wajen tsara fahimtar jama’a kan abubuwan da ke faruwa.”

Ya ci gaba da cewa, “Saboda haka nakan roƙi Majalisar Malamai su ci gaba da wa’azin zaman lafiya da kuma kira ga bin doka da oda a duk lokacin da dama ta samu. Wannan shi ne kawai hanyar da za mu iya cimma zaman lafiya da muke fata a Zamfara.”

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta samu gagarumar nasara a yaƙi da ’yan ta’adda, sai dai ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba.

Ya ce, “Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da tsaron jihar da dawowar cikakken zaman lafiya. Wannan aiki ne na haɗin kai — dole mu tashi gaba ɗaya mu fuskance shi tare.”

Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara
16 ga Oktoba, 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *