Gwamnatin Zamfara Ta Warware Matsalar Ɗaliban Ta Da Aka Bari A Indiya

Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Zamfara (ZSSB) ta bayyana cewa Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya amince da biyan bashin kuɗin karatun ɗaliban jihar da suka yi karatu a Jami’ar Sharda da ke ƙasar Indiya.

Wannan mataki, a cewar hukumar, ya zama wani muhimmin ci gaba wajen cika alƙawarin gwamnati na tallafa wa ilimi da ci gaban matasan jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ZSSB, Ahmed Haruna ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce, a baya dai, wasu ɗalibai ’yan asalin Zamfara an tura su jami’ar Sharda a ƙarƙashin tsohuwar gwamnati domin yin karatu a fannoni daban-daban, sai daga baya aka bar su ba tare da an biya musu kuɗin makaranta, da ba su masauki ba, lamarin da ya jefa su cikin ƙalubale yayin da suke ci gaba da karatunsu. Duk da haka, jami’ar ta nuna kyakkyawar alaƙa, ta bar ɗaliban su kammala karatu duk da waɗannan matsaloli.

A cewar sanarwar, gwamnatin Dauda Lawal ta shiga tsakani domin warware matsalar, bisa manufofin shirin ta na ceto Zamfara, ma’ana ‘Rescue Mission Agenda’. Dukkan ɗaliban da abin ya shafa yanzu an dawo da su gida lafiya, yayin da Gwamnan ya kuma amince da biyan duka kuɗin da aka tara a matsayin bashi, domin ba ɗaliban damar karɓar takardun shaidar kammala karatu ba tare da jinkiri ba.

Hukumar ta ce, wannan mataki zai bai wa waɗannan matasa sabuwar fata da ƙwarin gwiwa, tare da bai wa iyalan su natsuwa. Haka kuma zai ba su damar amfani da ƙwarewarsu wajen taimaka wa ci gaban Jihar Zamfara da ƙasar Nijeriya baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *