
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na gina jihar da ke tafiya bisa tsarin zamani mai dogaro da fasahar zamani.
A ranar Talata, gwamnan ya buɗe shirin horas da kwamfuta ga kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman, a fadar gwamnati da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa taron na horaswa wani muhimmin mataki ne da ke nuni da jajircewar gwamnatin jihar wajen sake fasalin Zamfara zuwa jiha mai ƙirƙirar sabbin abubuwa, gaskiya da ingantaccen aiki.

Sanarwar ta ce, wannan horo mai taken ‘Computer Appreciation Training’ an shirya shi ne ta Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), a matsayin babban taron ƙarawa juna sani ga manyan jami’an gwamnati.
A jawabinsa yayin buɗe shirin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan horo wata muhimmiyar hanya ce wajen cimma burin gwamnatinsa na ingantaccen aiki ta amfani da fasaha.
Ya ce, “Burin mu shi ne tabbatar da cewa kowane bangare na gwamnati yana aiki cikin tsari, inganci da sauri, kamar yadda fasaha ke bai wa duniya damar gudanar da aiki cikin sauƙi.
“Mun shiga wani zamani ne da fasaha ke sauya yadda ake gudanar da mulki – daga tsarin tsara manufofi, yanke shawara, zuwa yadda ake sadarwa da isar da ayyuka ga jama’a. A yau, sanin amfani da kwamfuta ba zaɓi ba ne, wajibi ne ga duk wanda ke aikin gwamnati.”
Gwamna Lawal ya ce, hukumar ZITDA ta ƙaddamar da muhimman shirye-shirye kamar Zamfara e-Governance Platform (e-GovConnect), tsarin Digital Literacy Framework, da kuma haɗin gwiwa da manyan kamfanonin fasaha na duniya don ƙarfafa ilimin fasaha a jihar.
Ya kuma buƙaci mahalarta da su ɗauki shirin da muhimmanci, yana mai cewa ilimin da za su samu a wajen zai taimaka wajen ƙara inganta aiki, gaskiya da ingantaccen hidima ga jama’a.
“Mutanenmu sun cancanci gwamnati mai wayewa kuma mai amsawa cikin gaggawa ga buƙatunsu. Wannan canjin kuwa, ‘yan uwa, yana farawa da mu. Bayan wannan shirin, za a gudanar da jarrabawa domin tantance abin da aka koya, wanda kuma zai zama wani bangare na kimanta aikin kowane jami’i,” in ji gwamnan.
Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
Oktoba 28, 2025
