Nijeriya ta nemi ƙarin haɗin gwiwar kafofin yaɗa labarai na ƙasashen D-8, ta zayyana sauye-sauyen da take samu a gida
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen nan da ake kira “Developing-8” (D-8) domin ƙarfafa tsarin kafafen watsa labarai, yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya, da kuma inganta haɗin kan yankin.
Ya yi wannan kira ne a cikin jawabin sa ga ministoci, shugabannin kafofin watsa labarai, da manyan masu tsara manufofi a taron ƙungiyar masu watsa labarai ta “D-8 Media Forum” wanda aka gudanar yau a Baku, babban birnin ƙasar Azerbaijan.
Yayin da yake magana kan taken taron, wato “Ƙarfafa Tattaunawa, Haɗin Gwiwa da Haɗin Kan Yanki,” ministan ya ce haɗin kai tsakanin ƙasashe masu tasowa a fannin yaɗa labarai da kafofin watsa labarai ya zama wajibi a wannan zamani da tsarin sadarwa na duniya yake canzawa cikin sauri sakamakon cigaban fasaha da kuma yawaitar labaran ƙarya.
Ministan, wanda Babban Sakataren Hukumar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NPC), Nze Dili Ezughah, ya wakilta, ya bayyana cewa kasancewar idan an haɗa kuɗin shiga na ƙasashen D-8 za a ga sun zarta dala tiriliyan 8, tare da kasuwancin tsakanin ƙasashen na aƙalla kashi 10 na kasuwancin duniya, haɗin kai a tsakanin kafafen watsa labarai yana taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa gaskiya, da tallafa wa cigaban ƙasashen.
Idris ya bayyana irin sababbin shirye-shirye da sauye-sauyen da Nijeriya ta aiwatar cikin shekarar da ta gabata, waɗanda ya ce suna ba da darussa na zahiri ga sauran ƙasashen da ke tasowa. Daga cikin su akwai kafa Cibiyar hukumar UNESCO ta “Media and Information Literacy” (Category 2)—ta farko a Afrika—wadda za ta zama cibiyar horo, bincike da tsaron dijital, domin bai wa ‘yan jarida da jama’a kayan aikin yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya.
Ministan ya buƙaci ƙasashen D-8 da su haɗa gwiwa da Nijeriya wajen ƙirƙirar kundin karatu, gina ƙwarewa, da gudanar da bincike tare.
Kasancewar an yi wa sama da mutane miliyan 100 rajistar shaidar dijital, Nijeriya ta samu cigaba a fannin tsarin shaidar dijital da kula da labarai, musamman wajen ƙarfafa amana a harkar mu’amalar dijital da inganta samun ayyuka ga jama’a na gwamnati.
Ministan ya ce tsarin shaidar dijital na Nijeriya zai iya taimaka wa ƙasashen D-8 wajen haɗa harkar kafofin watsa labarai da tsare-tsaren shaidar gaskiya domin rage yin kwaikwayo da yaɗa labaran ƙarya.
Yin la’akari da tasirin masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire a harkokin diflomasiyyar duniya, Idris ya haskaka gagarumin cigaban da masana’antar finafinai, kaɗe-kaɗe da labartattun bayanan dijital na Nijeriya suka samu.
Waɗannan masana’antu, tare da goyon bayan gyaran manufofi da cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, sun inganta martabar Nijeriya a idon duniya tare da samar da ayyukan yi ga matasa da dama.
Ministan ya bayyana yadda sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya—kamar gyaran tallafi da daidaita musayar kuɗi—suka inganta yanayin sadarwa ta hanyar bai wa rahotanni da bayanan gwamnati gaskiya da cikakken amana.
Idris ya lissafo wasu shawarwari don ƙarfafa haɗin kai a cikin ƙasashen na D-8 kamar haka:
• Gina tsarin ɗabi’u na bai-ɗaya ga kafofin watsa labarai na dijital.
• Ƙaddamar da shirye-shiryen koyar da kaifin fahimtar watsa labarai ga matasa, ‘yan jarida, masu tsara manufofi da kuma rukunin da ke cikin haɗari.
• Gudanar da binciken tare kan fasahar fasahar ƙirƙira (AI) a kafofin watsa labarai, musamman kayan aikin tantance gaskiya da tsaron dijital.
• Faɗaɗa musayar ƙwararru a kafofin watsa labarai, ɗaliban horo da haɗin gwiwar ɗakunan labarai tsakanin ƙasashe.
• Ƙarfafa haɗin kai a masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire da tsarin samar da abin dijital tsakanin membobin ƙasashen.
Ministan ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ci gaba da amfani da dabaru da mafita na cikin gida domin inganta zaman lafiya da cigaba a yankin.
Ya ce: “Nijeriya na ganin cewa D-8 ba wai ƙungiyar tattalin arziki ce kawai ba—al’umma ce ta ƙasashe masu ɗauke da buri iri ɗaya da matsalolin cigaba makamancin juna.
“Haɗin kan mu a fannin yaɗa labarai da kafofin watsa labarai yana da matuƙar muhimmanci wajen gina ‘yan ƙasa masu fahimta, al’ummomi masu haɗin kai da juna, da tattalin arzikin da ke da ƙarfi.”
Haka kuma ya jaddada cewa Nijeriya a shirye take ta yi aiki da ƙasashen D-8 domin ƙarfafa tattaunawa, gina amana a tsakanin jama’a, da inganta zaman lafiya.





