Tinubu ya naɗa Mohammed Idris cikin kwamitin yi wa Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu garambawul
Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ministoci shida wanda zai yi wa Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (NSIP) garambawul. Kafa kwamitin ya biyo bayan dakatar da shirin da Tinubu ya yi, mako ɗaya bayan dakatar da Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Dakta Betta Edu. Shugaban Ƙasar ya dakatar da Edu ne bayan sauke jagorar raba…
