Tag: Nijeriya
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta sha alwashin ƙarfafa dakarun tsaron Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana aniyarta ta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar, domin tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassa. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a yayin taron addu’o’i na musamman da aka shirya domin dakarun tsaron ƙasa a Babban Masallacin Juma’a na Ƙasa da ke Abuja. Shettima ya yaba…
Bayan Shekara Tara, Gwamnan Zamfara Ya Warware Matsalar Ɗaliban Jami’ar Crescent
Gwamna Lawal Ya Bai Wa Ɗalibai 50 Na Jami’ar Crescent Takardun Kammala Karatu Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa wa ɗalibai 50 takardun shaidar kammala karatu daga Jami’ar Crescent da ke Abeokuta, waɗanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin karatunsu a baya. An gudanar da taron miƙa takardun ne a ranar Alhamis a Babban Zauren…
Tinubu ya yaba wa kasuwar Musayar Hannayen Jari Ta Najeriya NGX bisa kai wa darajar Naira tiriliyan 100
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa kamfanonin Najeriya, ‘yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar hannun jari bisa nasarar da Kasuwar Musayar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX) ta kai darajar kasuwa ta Naira tiriliyan 100. A cikin wata sanarwar fadar shugaban ƙasa da mai ba shi shawara na musamman kan…
Ma’aikatar Tsaro Na Amfani Da Ofishin NSA Wajen Gallaza Wa ’Yan Adawa – Gwamnatin Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwar ta kan abin da ta kira amfani da ƙarfin Gwamnatin Tarayya wajen gallaza wa da tsoratar da ’yan adawa a jihar, tana mai cewa wannan al’amari na barazana ga dimokuraɗiyya da tsarin doka a Nijeriya. A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar,…
Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto jihar sa daga halin da take ciki, wato “Rescue Mission” yana tafiya yadda ya dace kuma yana haifar da gagarumin sakamako. A ranar Laraba, gwamnan ya kai ziyarar aiki a Ƙaramar Hukumar Shinkafi domin duba manyan ayyukan da gwamnatin jihar sa ke aiwatarwa a yankin….
Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ba da yawun sa wani hadimin sa mai suna Sa’idu Enagi ya yi wani rubutu kan siyasar Jihar Neja ba. Shi dai Enagi, ya wallafa sharhin ne a kafafen yaɗa labarai da taken “Malagi 2027”, inda ya yi wani hasashe kan wasu…
An tsara kasafin kuɗin 2026 don ƙarfafa nasarorin da shirye-shiryen Tinubu ke samu — Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa an tsara kasafin kuɗin 2026 ne domin ƙarfafa nasarorin da tsarin shirye-shiryen Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka fara samarwa, waɗanda tuni suka fara nuna sakamako mai kyau. Ministan ya bayyana hakan ne a wani sharhin sa da aka wallafa a jaridun ƙasar…
Tinubu, ba mutum ba ne wanda matsaloli ko ƙalubale suke firgita shi, cewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ba mutum ba ne wanda matsaloli ko ƙalubale suke firgita shi. Tsarin sa a kowane lokaci ya kasance cikin natsuwa da yanke shawara—yana mayar da ƙalubale wata dama don yin abubuwa mafi kyau da inganci. Hulɗoɗin mu na baya-bayan nan da Amurka shaida ne. A ƙarƙashin jagorancin sa, mun mayar…
Sarki Muhammadu Sanusi Ya Jinjina Wa CBN, Ya Ce Nijeriya Ta Tsallake Siraɗin Rugujewar Tattalin Arziki
Ashafa Murnai Barkiya Mai Martaba Sarkin Kano, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi Lamido, ya yaba wa hukumomin kula da harkokin kuɗi bisa matakan gaggawa da suka ɗauka wanda ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya a cikin shekarar da ta gabata. Sanusi ya ce a baya ƙasar ta fuskanci mummunan rashin…
