Daga Mujtaba Adam
Da aka yi wa wani jami’in gwamnatin Iran tambaya a kan yiwuwar sake buɗe yaƙi a tsakanin Isra’ila da Iran, sai ya bayar da jawabin cewa:
“ To dama wa ya ce an kawo ƙarshen yaƙin? Abin da ya faru shi ne tsagaita wuta kawai. Babu abin da zai hana sake dawowar yaƙi.
Wannan ne ya sa Iran a halin yanzu Iran take sake shiri domin fuskantar duk wani hatsari mai zuwa. Ta kuwa koyi darussa daga yaƙin kwanaki 12, musamman yadda manufar wannan yaƙin ya zama kashe dukkanin jagororin Iran da kuma kifar da gwamanti. Kuma babu dalili da zai tabbatar da cewa Amurka da Isra’ila sun dawo rakiyar wannan manufar.”
A can ƙasar abokan gaba ma bayanai suna fitowa da ba su kore yiwuwar buɗe sabon yaƙi ba. Tsohon ministan yaƙi, Avigdor Lieberman ya yi magana mai tasiri ga Isra’ilawa da ya faɗa wa wani Radiyo cewa: “Wani zangon na yaƙi da Iran yana karatowa.”
Sai kuma ya bai wa ‘yan sahayoniya shawarar da kar su yi nisa da dakunan buya da aka tanadi kayan buƙata a cikin su.
Wannan maganar da ta fito daga bakin Lieberman ta sa jami’an tsaron yahudawan suka fitar da gargaɗin da yake cewa:
“ Lieberman yana yin maganganu na haddasa hargitsi da kuma tsoratar da Isra’ilawa a kan Iran saboda kawai ya jawo hankulan mutane a kansa a ƙarƙashin gasar siyasa a tsakanin sa da ‘yan hamayya. Abin da yake yi abin takaici ne”.
Sai dai kuma Lieberman din bai daddara ba, ya ƙara furta wani zancen yana cewa:
“ Farkon yaƙi da Iran ya yi kyau matuƙa, mun kuma sami nasarorin da babu laifi. Amma kuma ba mu gama aiki ba. Mun raunanan Iraniyawa muka bar su a haka. Wannan kuma wannan abu ne mai hatsarin gaske. Wancan abin da ya faru, ya kamata a ce ya hana duk wani jami’i, yin barci na minshari.”
Sai dai kuma ba Lieberman ba ne kadai yake kaɗa kugen yaƙin Isra’ila a kan Iran ba. Natenyahu, wanda ya yi hira da ɗan jaridar Amurka, kuma ɗan Sahayoniya, Ben Shapir, ya bayyana cewa yaƙi da Iran bai ƙare ba.
Haka nan kuma ya so jawo hankalin ƙasashen Turai da Amurka a ƙoƙarin su taya shi yaƙi da cewa:
“ Iran tana ƙoƙarin kera makamai masu linzami da ke iya isa wata nahiya, kuma waɗanda za su iya ɗaukar makaman Nukiliya, da suke yi wa biranenku barazana. Suna kera makamai masu linzami da suke cin zangon kilomita 8000. Suna kuma da masu cin kilomita 3000. Za su iya kai bara da Nukiliya a kan biranen Newyork, Washington da Miami. Za kuma su iya isa Mar-a-Lago ( Garin Da Wurin Shakatawa Na Trump yake). Babu wanda yake son ganin mutanen da ke cewa: “Mutuwa Ga Amurka” suna iya tsinkayo ku.”
Kada kugen yaƙi da Lieberman da Netanyahu suke yi, ya sake jawo hankalin jami’an tsaron Isra’ilan suka sake fitar da bayani na rage damuwa a tsakanin Isra’ilawa. Dan Jaridar nan Ron Bin Yehsayi (ɗan sakon sojojin Isra’ila ) ya yi rubuta a jaridar “Yediot Ahranot.” Inda ya faɗi cewa:
“ Abin da cibiyar tsaro take faɗa a halin yanzu, shi ne babu wani dalili da yake nuni da cewa, Iran tana shirin kai hari a kan Isra’ila, ko kuma a ce tana tsare-tsaren yin hakan.”
Haka nan kuma ya ci gaba da cewa: “A halin yanzu Isra’ila ba ta da niyyar kai wa Iran hari, ko bude yaƙi da ita.”
Wasu kafafen watsa labaru suna cewa; Maganar Lieberman ba haka kawai ya yi ta ba. Domin Iran tana matuƙar ƙoƙarin sake gina tsarin tsaronta na sararin samaniya. Haka nan kuma tana sake gina cibiyoyinta na kera makamai masu linzami na “Ballistic” masu cin dogon zango.
Wani abu wanda yake tabbatacce shi ne cewa Isra’ila ta fahimci cewa, duk wani yaƙi da Iran ko da Lebanon a nan gaba, ba za ta iya yin shi ita kaɗai ba, sai idan Amurka ta taya ta. Taya ta kuwa da za ta yi, bai tsaya a cikin cewa ta ba ta bayanai na leƙen asiri da albarusai ba, tana son ta shiga ne kai tsaye a yi da ita. Shi ya sa Netanyahu yake fadin cewa; Abin da Isra’ila take yi, tana kare manufofin Amurka ne, ba maslaharta ita kaɗai ba.”