Ƙarin Harajin mai na 5% ba sabon haraji ba ne, kuma ba za a aiwatar da shi yanzu ba

Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsarin Haraji da Sauye-sauyen Haraji ya ce karin kashi 5% a kan farashin mai ba sabon haraji ba ne da gwamnatin Tinubu ta kawo.

A cewar kwamitin, wannan kudiri daman akwai shi a cikin dokar Federal Roads Maintenance Agency (FERMA) ta 2007, sai dai an sake saka shi a sabuwar dokar haraji ne domin samar da daidaito da kuma gaskiya.

Kwamitin ya ce karin ba zai fara aiki nan take ba har sai Ministan Kuɗi ya fitar da oda ta musamman a cikin sanarwar gwamnati.

Haka kuma, an bayyana cewa karin ba zai shafi dukkan kayan da ake saku daga man fetur ba, musamman wanda ake amfani da su a gidaje kamar gas ɗin girki (LPG), Kalanzir, da CNG, domin tallafawa burin Najeriya na wanzar da makamashi mai tsafta.

Kwamitin ya ce an samar da karin kuɗin ne domin samar da kuɗaɗen ginawa da gyaran manyan hanyoyi. Ya ce idan an aiwatar da shi yadda ya kamata, zai rage yawaitar aukuwar haɗari a hanya, zai sauƙaƙawa matafiya, da kuma rage kuɗin sufuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *