Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana goyon bayanta ga cikakken ikon Najeriya kan harkokinta na cikin gida tare da tabbatar da ’yancin addini da bin doka da oda a kasar.
A wata sanarwa da Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ta fitar, ta jaddada cewa tana da cikakken kishin kiyaye dokokin da ke cikin kundin kafa kungiyar, musamman kan batun ikon kasa, rashin katsalandan, da ’yancin addini.
Hukumar ta ce ta damu da wasu kalamai daga gwamnatin Amurka da ke zargin gwamnatin Najeriya da hannu wajen kashe mabiya addinin Kirista a kasar, da kuma barazanar kai farmakin soja kan kasar.
A cewar sanarwar, Najeriya na daga cikin mambobin AU masu muhimmanci wadanda ke taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, yaki da ta’addanci, da hadin kai a nahiyar.
“AU tana mutunta cikakken ikon Najeriya wajen tafiyar da lamurran tsaronta, tsaron kasa, da ’yancin addini bisa tsarin kundin mulki da ka’idojin kasa da kasa,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce ta amince da matsayar da gwamnatin Najeriya ta sha nanatawa cewa kundin tsarin mulkin kasar yana baiwa kowane dan kasa ’yancin yin addinin da yake so, kuma gwamnati ba ta amince da wani nau’in wariya ko zaluncin addini ba.
Ta kuma jaddada cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta na da sarkakiya, suna shafar mabiya addinai daban-daban, ciki har da matsalar ta’addanci, satar mutane, rikicin kabilanci da rikicin makiyaya da manoma.
Hukumar ta yi kira da a kara hadin kai tsakanin kasashen yankin da abokan hulɗa na kasa da kasa domin taimakawa Najeriya da sauran kasashen Afirka wajen karfafa matakan tsaro, kare rayuka, da gurfanar da masu aikata laifuka.
“Ya zama wajibi a guji amfani da addini a matsayin makami na siyasa ko bayanin da zai iya haifar da rikici,” in ji AUC.
Hukumar ta kuma bukaci kasashen waje, musamman Amurka, da su ci gaba da tattaunawa da Najeriya ta hanyar diflomasiyya, musayar bayanan tsaro, da taimakon ci gaban ƙwarewa maimakon barazanar kai farmaki, wanda ka iya barazana ga zaman lafiyar nahiyar.
A karshe, Hukumar Tarayyar Afirka ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafawa kasashen mambobinta wajen tabbatar da zaman lafiya, kare hakkin dan Adam, da cigaban tattalin arziki, tare da mutunta ikon kowace kasa da ka’idar rashin tsoma baki.
