Hukumar ba da lamunin karatu ta NELFUND (Nigerian Education Loan Fund) ta ce adadin ɗaliban da suka amfana da lamunin karatu tun bayan ƙaddamar da shirin a ranar 24 ga Mayu 2024 ya kai 788,947.
Wannan na cikin rahoton yau da kullum da hukumar ta fitar a ranar 24 ga Nuwamba 2025, wanda ya kuma nuna cewa an karɓi rejistar ɗalibai 1,161,531 masu neman lamuni tun lokacin da aka buɗe shafin yanar gizon shirin.
A cewar rahoton, an samu ƙarin masu nema har mutum 4,076 a cikin rana guda, wanda ke wakiltar 0.4% na sabbin ɗalibai da aka samu.
Ya zuwa ranar 12 ga Nuwamba 2025, an biya jami’o’i da makarantun gaba da sakandare 262 kuɗin karatu da suka kai Naira Biliyan 82,346,711,374. An kuma biya ɗalibai kuɗin tallafin yau da gobe da suka kai Naira Biliyan 58,537,760,000. Jimillar kuɗin da aka raba gaba ɗaya ya kai Naira Biliyan 140,884,471,374.
NELFUND ta ce wannan ci gaba na daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen tallafawa ɗalibai da ƙarfafa ilimi a faɗin ƙasar.
Hukumar ta kuma jaddada cewa shirin lamuni zai ci gaba da ba da dama ga ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi domin samun ilimi ba tare da cikas ba, tare da tabbatar da biyan kuɗin karatu kai tsaye ga makarantun da suka dace.
