Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon shafin intanet don inganta sayayya a ma’aikatun gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin magance matsalolin da suka dabaibaye harkar sayayya a hukumomin gwamnati tare da ƙara inganta ayyuka a ma’aikatun gwamnati. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba yayin ƙaddamar da Gidan Yanar Takardun Shaidar Sayen Kaya na Nijeriya da Hukumar…
