Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki kan bashin da ake bin bangaren wutar lantarki na Naira tiriliyan 4
Wata sanarwa da mai bada shawara na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a na ministan makamashi Adebayo Adelabu, wato Bolaji Tunji ya fitar a ranar Lahadin, ta ce gwamnatin tarayya ta sha alwashin yin gaggawar magance basussukan, biyo bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin Adelabu da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki…
