Ministan Yaɗa Labarai Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da kamfen na wayar da kan ɗaliban makarantun sakandare kan kafofin sadarwa da yadda ake amfani da su ta hanyar da ta dace. Da yake jawabi a taron TEDxNTICAbujaYouth 2025 da aka gudanar a makarantar Nigerian Tulip International College, Abuja, a ranar Asabar,…
