UNGA80: Najeriya ta nemi a yafe bashi ga ƙasashen da ake bi da ba da damar yin kasuwanci domin samun ci gaba mai ɗorewa
Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su yafe bashi ga ƙasashe masu tasowa, yana mai cewa hakan hanya ce madaidaiciya ta wanzar da zaman lafiya da ci gaba. Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ƙasa…
