Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara na Naira Biliyan 140
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai kusan Naira Biliyan 140 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, a wani shiri da aka bayyana a matsayin sabon babi na farfaɗowa da ci gaban Zamfara. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, Kwamishinan Yaɗa…
