Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin ‘yan jarida bakwai na Gombe da suka rasu a haɗarin mota
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan rasuwar wasu ‘yan jarida bakwai a wani mummunan haɗarin mota guda ɗaya da ya faru a yankin Gombe ta Kudu, Jihar Gombe, a ranar Litinin. Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin yayin da ‘yan jaridar suke dawowa…
