Shirye-shiryen Tinubu na ƙarfafa matasa na kowane ɗan Nijeriya ne, ba na muradun siyasa ba – Idris
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa shirye-shiryen ƙarfafa matasa na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu suna fitowa ne daga sahihin ƙudirin faɗaɗa damarmaki ga matasan Nijeriya, ba wai saboda la’akari da siyasar jam’iyya ba. Idris ya yi wannan bayani ne a daren Talata a Abuja, yayin wani taron mu’amala…
