Haƙuri da addinin juna shi ne jigon zaman lafiya da haɗin kan Nijeriya – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, haƙurin addini, da zaman lafiya, yana mai bayyana su a matsayin muhimman ginshiƙan tsaron ƙasa da ci gaba mai ɗorewa. Shugaban Ƙasar ya yi kiran ne a wurin taron ƙasa da ƙasa karo na huɗu na Cibiyar Wayewar Musulunci…
