Shugaba Tinubu Ya Jajanta wa ‘Yan Kasuwar Kano Kan Gobarar Kasuwar Singer, Ya Ba da Umarnin Bincike
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa ‘yan kasuwa da al’ummar Jihar Kano sakamakon gobarar da ta tashi a Kasuwar Singer a ƙarshen makon nan. Gobarar, wadda ta fara da yammacin ranar Asabar, ta ci gaba da ƙonewa har zuwa safiyar Lahadi, inda ta haddasa mummunar asara musamman a sashen sayar da kayan abinci…
