Gwamnatin Tarayya ta fara sabunta kayan aikin gidajen watsa labarai, cewar Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara zuba jari wajen samar da sababbin fasahohi da na’urorin zamani domin ƙarfafa ayyukan kafafen yaɗa labarai na gwamnati.

Ya bayyana hakan ne a birnin Las Vegas da ke Jihar Nevada ta ƙasar Amurka yayin wata tattaunawa da manyan kamfanonin watsa shirye-shirye a taron Ƙungiyar Ƙasa ta Masu Watsa Shirye-shirye (NAB) 2025 da aka gudanar.

Ya ce wannan zuba jarin zai taimaka wajen sabunta da kuma maye gurbin tsofaffin kayan aiki a tashoshin rediyo da talabijin na Gwamnatin Tarayya.

Domin cimma wannan buri, ministan ya bayyana cewa ma’aikatar sa tana haɗin gwiwa da masana’antun kayan watsa shirye-shirye domin bai wa ‘yan jarida a cikin gida damar cin gajiyar sababbin fasahohi da horo na musamman da ya shafi sana’ar su.

Ministan ya jaddada ƙudirin Gwamnati na yin aiki tare da muhimman abokan hulɗa a fannin watsa labarai da sadarwa a duniya domin ƙarfafa tsarin yaɗa labarai a Nijeriya.

Ya ce: “Sadarwa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa manufofin Ajandar Sabunta Fata sun isa ga al’ummar Nijeriya yadda ya kamata.”

A yayin taron, Minista ya kai ziyara wuraren da ake baje-kolin kayayyakin zamani da suka haɗa da eriyoyi, na’urorin aika sigina (tiransimita), da kayan aikin situdiyo – duk waɗanda ke da matuƙar muhimmanci wajen inganta watsa shirye-shirye.

Waɗansu daga cikin shugabannin kamfanonin da suka gana da ministan sun haɗa da Shugaban KINTRONIC Laboratories, Thomas King; da Shugaban Axel Technology SRL, Enrico Vaccari; da Shugaban SYES SRL, Gianluca Baccalini; da Shugaban Kintronic Labs Inc, Josh King; Shugaban Thomson Broadcast, Khiran Keerodhur, da Shugaban Continental Electronics, Calvin Carter.

Dukkan su sun nuna a shirye suke su haɗa gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin haɓaka harkar watsa labarai da kuma ƙarfafa hukumomin da ke da alhakin tsarawa da sa ido.

A tawagar da Idris ya jagoranta zuwa Amurka ɗin akwai manyan jami’an hukumomin yaɗa labarai na Nijeriya da suka haɗa da Darakta-Janar na NTA, Salihu Abdulhamid Dembos; Manajan-Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Ali Muhammad Ali; Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tashoshin Rediyo da Talbijin (NBC), Charles Ebuebu; Shugaban Hukumar Kula da Harkar Tallace-Tallace ta Ƙasa, (ARCON), Dakta Lekan Fadolapo; da Darakta-Janar na tashar Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace.

Idris a tsakiyar wasu jami’an da ya yi tafiyar da su

Taron na NAB, wanda aka gudanar daga ranakun 5 zuwa 9 ga Afrilu, 2025, yana da taken, “Fasaha, Salo da Makoma”, inda aka tattauna batutuwan zamani kamar Ƙirƙirarriyar Basira (AI), bayyanar bayanai ta hanyar fasahar girgije, tattalin arzikin masu ƙirƙira, da kuma samar da shirye-shiryen wasanni da watsa su ta intanet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *