Haɗin kai tsakanin Gwamnati da Majalisa ya haifar da manyan Nasarori a cikin shekaru 2 -Shugaba Tinubu

A wani bangare mai karfi na jawabin sa a yayin zaman hadin gwiwar Majalisar Tarayya domin bikin Ranar Dimokuradiyya, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar godiya da yabo ga ‘yan majalisar tarayya bisa yadda suka bayar da cikakken hadin kai ga bangaren zartaswa tun bayan hawansa mulki.

Shugaban kasar ya ce:
“A cikin shekara guda da muka yi tare, Majalisar Tarayya ta tabbatar da cewa hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati yana da matukar muhimmanci wajen sauke nauyin da ke kanmu.”

Tinubu ya jaddada cewa hadin kan ya kawo sauyi mai dorewa ga kasa, ya kuma taimaka wajen tabbatar da dimokuradiyya mai ma’ana da kima. Ya yabawa Majalisar akan saurin amincewa da manyan dokoki da suka dace da ci gaban kasa da kare muradun ‘yan kasa, ciki har da dokokin tattalin arziki, tsaro, da kiwon lafiya.

“Wannan Majalisa ba ta zama abokiyar adawa ba, ta zama abokiyar hadin kai domin cigaban kasa, ba don jam’iyya ba.” Inji shi

Ya ƙara da cewa, wannan dangantaka mai kyau da Majalisa ta kara tabbatar da cewa Najeriya tana kokarin kulla sabuwar al’adar siyasa wadda ke girmama doka da tsarin mulki, tare da nufin samar da cigaba mai ma’ana ga al’umma.

Shugaba Tinubu ya kuma yi kira ga ci gaba da irin wannan hadin kai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa na da niyyar tafiya kafada da kafada da bangaren dokoki don cimma burin al’ummar Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *