Tinubu: Gwamnati Za Ta Kara Kaimi Wajen Kawar da ’Yan Ta’adda da tabbatar da Tsaron Ma’aikata

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwa da alhini bisa harin kunar bakin wake da aka kai a Konduga, Jihar Borno.

Shugaba Tinubu ya bayyana harin a matsayin zalunci na rashin imani, yana mai cewa hakan ba zai hana gwamnati da hukumomin tsaro ci gaba da fatattakar ragowar ’yan ta’addan Boko Haram ba, waɗanda ke kai hare-hare ga al’umma don karkatar da hankali daga raunansu a fagen fama.

Shugaban Ƙasa ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Borno da al’ummar jihar bisa wannan mummunar ta’addanci. Haka kuma, ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta gaggauta kai ɗauki da taimako ga waɗanda suka jikkata da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

A gefe guda kuma, Shugaba Tinubu ya bayyana alhini da jimamin sa sakamakon fashewar wani abu a wani kamfanin rodi a Jihar Kano a safiyar Asabar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar, yayin da wasu goma suka jikkata.

Shugaban ya bada umarnin a ɗauki matakin gaggawa wajen tabbatar da tsaron ma’aikata da lafiyar muhallai a irin waɗannan wurare. Ya kuma umarci hukumomin gwamnati masu alhakin kula da masana’antu da tsaron muhalli da su gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin fashewar da ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *