Gwamnatin Tarayya Ta Bada Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja Duk da Gargaɗin Da Ofishin Jakadancin Amurka Ya Ba Matafiya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin cewa Babban Birnin Tarayya Abuja yana da tsaro ga mazauna cikin sa da baƙi da kuma jakadun ƙasashen waje.

Wannan tabbacin na zuwa ne bayan da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya fitar da wata sabuwar sanarwa kan tsaro, inda ya hana tafiye-tafiyen ma’aikatan sa da iyalan su zuwa wuraren soja ko wasu gine-ginen gwamnati a Abuja, in ba don ayyuka na hukuma ba.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin kowane ofishin jakadanci na fitar da irin wannan gargaɗi ga ‘yan ƙasar sa, sai dai ya jaddada cewa babu wani haɗari na kai-tsaye a Abuja.

Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.”

Ya bayyana cewa hukumomin tsaro a Nijeriya suna aiki tuƙuru dare da rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya ƙara da cewa tsarin tsaro a Abuja yana aiki yadda ya kamata tare da nasarori masu yawa wajen gano duk wata barazana da kuma daƙile ta kafin ta faru.

Ministan ya ƙara da cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ba ya nuni da wata barazana kai-tsaye ga Abuja, illa ya dogara ne da al’amuran tsaro na duniya gaba ɗaya.

Ya ce: “Mun fahimci cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ya ta’allaƙa ne da wasu abubuwan da ke faruwa a duniya gaba ɗaya, ba wai yana nuna wata barazana kai-tsaye ko ta gaggawa a cikin Babban Birnin Tarayya ba.

“Sai dai muna sake jaddadawa ga dukkan ofisoshin jakadanci, da masu zuba jari da abokan cigaba, da jama’a gaba ɗaya cewa babu wani dalilin fargaba.”

Ya kuma bayyana ƙudirin gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a birnin tarayya, yana mai cewa: “Gwamnatin Tarayya tana son sake jaddada ƙudirin ta na kare lafiyar duk mazauna ƙasar nan tare da ci gaba da tabbatar da martabar Abuja a matsayin ɗaya daga cikin manyan biranen da suka fi tsaro a duniya.”

Daga ƙarshe, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba, tare da yin taka-tsantsan da kuma bayar da rahoto kan duk wani abu da suka ga ya ɗaure masu kai ga jami’an tsaro mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *