A kokarinsa na farfado da harkar noma a Najeriya, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin Renewed Hope Agricultural Mechanisation Programme tare da mika taraktoci 2,000 da kayan aikin noma ga manoma a fadin kasar nan.
An gudanar da taron a hedikwatar Hukumar Sarrafa Irinn Gona ta Kasa (National Agricultural Seeds Council), dake Sheda, a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Shugaba Tinubu ya bayyana wannan shirin a matsayin wata alamar sauyi da zata ceto Najeriya daga dogaro da abinci daga kasashen waje, yana mai cewa:
“Mun yi alkawari, kuma yanzu muna cika shi. Wannan shine matakin farko na sauya fasalin noma a kasar nan. Najeriya na da kasa mai albarka, mutane masu himma, da dabarun fasaha. Lokaci ya yi da za mu tsare kanmu a fannin abinci.”
Shugaban kasa ya bayyana cewa wannan shiri zai saukaka wa manoma, musamman kanana, wajen samun damar amfani da na’urorin zamani da rage wahalar aiki da kara yawan amfanin gona. Ya kara da cewa za a raba taraktocin da tabbatar da adalci da inganci.
Shugaba Tinubu ya yabawa hadin gwiwar da gwamnatin kasar Belarus ta bayar wajen samar da na’urorin, horar da matasa, da kuma sauya fasahar kere-kere a Najeriya. Ya bayyana Alex Sigman, wani abokin karatunsa a Jami’ar Chicago daga Belarus, a matsayin wanda ya saukaka cimma wannan yarjejeniya.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa wannan shirin ya kunshi taraktoci 2,000, na’urorin hada girbin amfanin gona guda 10, taron bita da karin ilimi sau 12, da kayan gyaran na’urorin guda 9,000. Ya kara da cewa an tsara shirin don sarrafa fiye da hekta 550,000 na gonaki, samar da metric ton 2,000,000 na abinci, da kirkiro guraben ayyuka fiye da 16,000.
“Ba a taba ganin irin wannan shiri na zamani a bangaren noma a tarihin Najeriya ba. Wannan shine mafi girma da doka da tsari,” in ji Kyari.
Daga cikin manyan baki a wajen taron akwai: Shugaban APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje; Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago; wakilai daga Majalisar Dokoki da kungiyar manoma, da sauran abokan hulda na ci gaban noma.