Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta yi shirin kafa cibiyoyin kiwon shanu a dukkan yankuna shida na ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Noma, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a rana ta biyu ta taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, da kuma nazarin rabin wa’adin mulkin Tinubu.
Taron, wanda Gidauniyar Sa Ahmadu Bello ta shirya, yana gudana ne a Gidan Arewa, a Kaduna.
A cewar ministan: “Aikin haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin Ma’aikatun Noma, Muhalli, Albarkatun Ruwa, Bunƙasa Kiwon Dabbobi da kuma Tattalin Arzikin Ruwa yana da matuƙar muhimmanci domin cika manufofin Ajandar Sabunta Fata.”