Gwamnatin Tarayya ta bayyana jimamin ta kan mummunar gobarar da ta auku a bene mai suna Afriland Towers da ke Titin Broad, a Legas, ranar Talata, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane goma daga cikin manyan jami’an Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kamfanin United Capital PLC (UCP), tare da jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: “Wannan babban rashi ne mai matuƙar raɗaɗi da girgiza zuciya, ba kawai ga iyalai da hukumomin da abin ya shafa kai-tsaye ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“Muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga iyalan mamatan, da abokan aikin su da abokan su, haka kuma ga FIRS da UCP.
“Muna yi wa duk waɗanda suka samu rauni addu’a da fatan samun cikakkiyar lafiya cikin gaggawa.”
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Legas don tabbatar da an gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana maimaituwar sa a nan gaba.
“Allah Maɗaukaki ya ba wa iyalan da abin ya shafa haƙuri, ya warkar da waɗanda suka jikkata, ya kuma ba wa ƙasar nan ƙarfin jure wa wannan babban rashi,” inji shi.