Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada bukatar a bai wa Najeriya kujerar dindindin a Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a matsayin ɓangare na sauye-sauyen da ake son yi wa tsarin majalisar.
Tinubu, wanda Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a zauren tattaunawa na babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.
“Ya zama dole Najeriya ɓ ta samu kujerar dindindin a Kwamitin tsaro. Wannan wani muhimmin ɓangare ne na sauye-sauye domin dawo da amincewa ga wannan hukuma, wacce ita ce ginshikin tsarin haɗin gwiwa na duniya,” in ji shi.
Shugaban ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta dawo da martabarta ne kawai idan ta dace da yanayin duniya na yanzu, ba ta bar tarihi ya daure ta ba.
Ya bayyana cewa lokacin da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya, Najeriya ƙasa ce ƙarƙashin mulkin mallaka mai mutane miliyan 20, ba tare da samun wakilci a teburin da ake yanke hukunci kan makomarta ba.
“Yanzu kuwa, mu ƙasa ce mai ‘yanci, muna da fiye da mutane miliyan 236, kuma an yi hasashen nan da shekaru masu zuwa mu zama ƙasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya. Najeriya ta dade tana zama ginshikin tsaro a nahiyar Afirka, kuma abar dogaro a aikin kiyaye zaman lafiya na duniya,” in ji Tinubu.
Ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun taka rawa a cikin ayyuka 51 daga cikin 60 na kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar tun bayan samun ‘yancin kai a 1960.
Shugaban ya kuma ce ƙasar ba ta tsaya ga kanta ba wajen yakar ta’addanci, inda ta yi aiki tare da makotan ƙasashen Afirka ta hanyar Multinational Joint Task Force (MNJTF).
Tinubu ya ce Najeriya ta koyi darasi daga doguwar gwagwarmaya da ta yi da ƙungiyoyin tsattsauran ra’ayi.
Ya kuma ce dalilin da ya sa Najeriya ke magana kan rikicin Gaza, harin da aka kai Qatar da sauran tashin hankula a yankin shi ne saboda ƙwarewar da ƙasar ta samu daga irin wannan rikice-rikice da ba sa ƙarewa inda aka fara.
Shugaban ya ƙara da cewa Najeriya tana goyon baya ga shirin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na UN80 Initiative, wanda ya yi kira da a sauya tsarin hukumar domin ya dace da zamani, a kuma kawo ƙarshen maimaita ayyuka da ɓata kuɗi.