Tinubu: Najeriya Na Kan Hanyar Kai Wa Ga Ƙarfin Tattalin Arziƙi Mai Ɗorewa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin arzikin ƙasar ya soma dawowa daidai sakamakon manufofin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar.

Shugaban ya bayyana haka ne a Ibadan, lokacin bikin naɗa Oba Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadanland. Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya bayyana farin cikinsa da yadda ‘yan Najeriya suka nuna haƙuri da goyon baya a lokacin aiwatar da manufofin.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa tattalin arzikinmu ya soma gyaruwa, kuma yanzu akwai haske,” in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma yaba da rawar da sabon Olubadan ya taka a tarihin siyasar Najeriya, musamman yadda ya tsallake ƙoƙarin tsige shi daga kujerar gwamnan Jihar Oyo a baya. Ya bayyana shi a matsayin wata alama ta juriyar shugabanci da sadaukarwa ga jama’a.

A wajen bikin, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya mika wa Oba Ladoja sandar iko da takardar shaidar zama Olubadan. Ya ce hakan ya kawo ƙarshen jayayya tsakanin dangin sarautar Ibadan.

A jawabinsa, sabon Olubadan ya bayyana nadin nasa a matsayin hukuncin Allah, tare da gode wa shugaban ƙasa da gwamnan jihar bisa girmamawa da goyon baya.

Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin akwai gwamnonin jihohin Ondo, Ekiti, da Osun, tsofaffin gwamnonin Cross River, Osun, Kano da Ogun, tare da shugabannin gargajiya ciki har da Sultan na Sokoto, Alaafin na Oyo da Soun na Ogbomoso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *