Najeriya @65: Mun samu gagarumin ci gaba a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da kalubalen tattalin arziki da tsaro da kasar ta fuskanta.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce manufofi da matakan da aka dauka sun fara sauya akalar tattalin arzikin kasar.

Karuwar kudaden shiga da rage bashi

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta samu karin kudaden shiga daga albarkatun da ba na man fetur ba, inda a bana kadai aka tara fiye da Naira tiriliyan 20. A cewar sa, adadin da ake kashewa wajen biyan bashin da ake ci ya ragu daga kusan kashi 97% zuwa kasa da 50%.

Farfaɗowar Tattalin arziki

Rahoton hukumar kididdiga ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu karuwar kashi 4.23% a zangon biyu na shekarar 2025, wanda ya zarce hasashen IMF na kashi 3.4. Haka kuma, hauhawar farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 20.12% a watan Agusta, mafi karanci cikin shekaru uku.

Ci gaban masana’antu da kasuwanci

Shugaban ya ce Najeriya ta koma “net exporter”, wato tana sayar da kaya ga ƙasashen waje fiye da yadda take saya daga garesu. A cewar sa, kayayyakin da aka kera a gida Najeriya sun karu da kashi 173%, kuma kusan rabin abin da ake fitarwa yanzu ba man fetur ba ne.

Ya kara da cewa samar da danyen mai ya karu daga ganga kasa da miliyan daya a rana a shekarar 2023 zuwa ganga miliyan 1.68, yayin da a karon farko cikin shekaru 40 aka fara tace man fetur a cikin gida.

Asusun ajiyar ƙada da darajar Naira

Shugaba Tinubu ya ce asusun ajiyar kasar ya karu zuwa dala biliyan 42.03, mafi girma tun 2019. Ya kuma ce Naira ta farfado bayan rikicewar da ta shiga a 2023–2024, inda gibin farashin gwamnati da na kasuwar bayan-fage ya ragu sosai.

Shirye-shiryen tallafi ga talakawa

Gwamnati ta raba Naira biliyan 330 ga iyalai miliyan takwas a karkashin shirye-shiryen tallafin zamantakewa. Haka kuma, matasa sama da 153,000 sun amfana da lamunin Credicorp, yayin da daruruwan dubban dalibai suka samu lamunin karatu ta ƙarƙashin shirin NELFUND.

Ababen more rayuwa

A bangaren gina kasa, gwamnati ta ce ta ci gaba da manyan ayyuka kamar layin dogo na Kaduna–Kano da Kano–Katsina–Maradi, titin Lagos–Calabar Coastal Highway, da kuma titin Sokoto–Badagry.

Tsaro

Shugaban ya ce jami’an tsaro na ci gaba da nasara a yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas da IPOB a Kudu maso Gabas. Ya ce zaman lafiya ya fara dawowa a wasu sassan da rikice-rikice suka daɗe suna addabawa.

Matasa da kirkire-kirkire

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati na cigaba da zuba jari a matasa ta hanyar shirye-shiryen inganta kirkire-kirkire da fasaha, ciki har da shirin iDICE programme, wanda zai tallafa wa masu fara sana’o’i ta intanet da kere-kere.

“Lokacin sabuwar Najeriya ya zo”

Shugaban ya ce duk da radadin da ’yan Najeriya suka fuskanta sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki, sakamakon ya fara bayyana.
“Ina tabbatar muku da cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta zama kasa mai dogaro da kanta, mai arziki, da alfahari da kanta,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *