Nijeriya ta biya bashin Dala biliyan 2.86 cikin watanni takwas -CBN

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatar da cewa an biya basussukan waje na adadin Dalar Amurka biliyan 2.86, daga Janairu zuwa Agusta, 2025.

Bayanin yana cikin wasu alƙaluman ƙididdigar bayanan kuɗaɗe, wanda CBN ya fitar cikin wannan mako.

Idan za a tuna daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2024 da ta gabata kuwa, Nijeriya ta biya bashin Dala biliyan 3.06.

Wannan bashi da aka biya dai a cikin 2025, yana nufin duk wata Dala 10 da ta fita daga Nijeriya, to kusan Dala 7 na tafiya ne wurin biyan bashi a ƙasashen waje.

A cikin watan Janairu 2025, an biya bashin Dala miliyan 540.67. A cikin watan Fabrairu kuma aka biya Dala miliyan 276.73.

An biya har Dala miliyan 632.36 a cikin watan Maris. A cikin Afrilu an biya Dala miliyan 557.76, sai kuma cikin Mayu da aka biya Dala miliyan 230.92.

Adadin bashin da Nijeriya ta biya cikin watan Yuni ba shi da yawa. An biya Dala miliyan 143.39. A watan Yuli kuma aka biya Dala miliyan 176.95. Cikin Agusta 2025 kuma aka biya Dala 302.3.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *