Yadda CBN Ke Tallabe Da Tattalin Arzikin Nijeriya, Yayin Da Farashin Ɗanyen Mai Ke Faɗuwar-‘yan-bori A Kasuwa

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Yayin da farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a duniya, yanzu haka ganga ɗaya ta ɗanyen mai kaɗan ta haura Dala 64. Haka kuwa ga ƙasar da tattalin arzikin ta ya dogara ga kuɗin fetur kamar Nijeriya, babbar barazana ce ba samun sauƙi ba. Wani hasashe da mujallar The World Street Journal ta buga cikin wannan makon, ya nuna cewa ɗanyen mai samfurin Brent mai ƙaramar daraja zai ƙara yin ƙasa zuwa Dala 50 nan zuwa ƙarshen 2025. Hakan kuwa ya nuna buƙatar tashi tsaye domin samar da dabarun hanyoyin hana tattalin arziki afkawa cikin dawurwura.

Domin kauce wa hakan, tuni Babban Bankin Nijeriya (CBN), a ƙarƙashin Gwamnan Banki, Olayemi Cardoso, ya bijiro da hanyoyin da za su ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida a yayin da darajar farashin ɗanyen mai ke faɗuwa.

Kasafin Kuɗaɗen Nijeriya na 2025 ya dogara ne kan hasashen cewa za a riƙa haƙo ganga miliyan 2 a kowace rana, kuma an shata kasafin kan hasashen za a riƙa sayar da kowace gangar ɗanyen mai kan Dala 75. To yanzu kuwa akwai damuwa, domin farashin ɗanyen mai ya faɗi warwas, lamarin da ka iya haifar da wawakeken giɓin kusan kashi 7 bisa 100 na Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP), wanda hakan ka iya haifar da tsadar rayuwa da ta hauhawar farashi.

To sai dai kuma Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fito da wasu tsare-tsaren da za su hana matsalar faɗuwar farashin ɗanyen mai ta shafi tattalin arzikin cikin gida na Nijeriya. Daga cikin waɗannan tsare-tsaren akwai batun bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga waɗanda ba na ribar ɗanyen mai ba, ƙarfafa hanyoyin rage dogaro da kayan da ake shigowa da su daga waje, sai kuma zaburar da hanyoyin da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje za su riƙa shigo da kuɗaɗen waje cikin ƙasar nan, domin a samu yawaitar su.

A ɓangaren amfanin gona za a inganta fitar da kayan da aka sarrafa, maimakon yawan fitar da tsabar amfanin gona waje. Haka zai sa a ƙarfafa sassafa kayayyakin amfanin jama’a a cikin ƙasa. Sannan kuma za a rage shigo da kayayyaki masu tsada. Cardoso ya ce wannan shiri ya bijiro da hanyoyin samun kuɗaɗe da dama, yadda tattalin arziki zai ƙaru da Dala biliyan 25 a kowace shekara.

Kwanan nan kuma Cardoso ya shawarci masu kamfanonin layukan waya irin su Airtel, MTN da sauran cewa su riƙa buga kayayyakin su kamar layin waya, wato ‘sim cards’ a cikin ƙasar nan, maimakon bugawa a waje. Ya ce yin haka zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin cikin gida.

Yayin da yake jawabi lokacin da Shugaban kamfanin Airtel Africa, Sunil Taldar ya kai masa ziyara, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya ya bayyana masa muhimmancin ƙarfafa sarrafa kayan su a cikin gida. Idan suka yi haka, Cardoso ya ce za a rage tsananin buƙatar Dala a cikin gida, domin kamfanonin na ɗaya daga cikin manyan masu buƙatar Dala afujajan domin fita da kuɗaɗen su buga kayayyakin kasuwancin su a waje, sannan su shigo da shi cikin ƙasar nan, musamman katin lambar waya, kebura na wayoyin ‘cables’ da hasumiyar ƙara nisan zangon masu iya kiran lambobin su. Duk waɗannan kuwa daga waje ake shigo da su. Saboda haka shi ma shugaban na kamfanin Airtel ya yi na’am da wannan shawara da Gwamnan CBN ya ba shi. Wasu hanyoyin da CBN ke bi sun haɗa ci gaba da farfaɗo da darajar Naira a hada-hadar musayar kuɗaɗen waje, abin da ke ƙara sa masu zuba jari daga waje ke ƙara yin amanna da gamsuwa ana zuba jari a Nijeriya. A yanzu haka Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Wajen Nijeriya ya haura Dala biliyan 43.4, cikar da a baya bai taɓa yin irin ta baƙil ba.

Hasashe ya tabbatar da cewa farashin ɗanyen mai zai iya ƙara faɗuwa idan ƙasashen OPEC suka yi shawarar ƙara yawan ɗanyen man da suke haƙowa a kullum, a taron da za su yi cikin Nuwamba 2025 ɗin nan.

Dambarwa da kwatagwangwamar siyasar kasuwanci da ake yi tsakanin Amurka da China ce ta ruruta wannan matsala. Ita dai China ta daina sayen ɗanyen mai daga Amurka tun a cikin watan Mayu 2025. Rabon da ta sayi gas daga Amurka kuwa tun cikin watan Fabrairu 2025. Ita da Indiya sun fi karkata da cinikayya da Rasha a yanzu. Duk da a sabuwar yarjejeniyar kasuwancin da ƙasashen biyu, wato Amurka da Rasha suka sake ƙullawa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce lallai sai dai Chana ta ci gaba da sayen ɗanyen mai da gas daga Amurka. Amma har yanzu dai ko ɗanyen mai cikin bokitin fenti ɗaya ba ta fara saye daga Amurka ba. Haka bayanan ƙididdigar kasuwanci na duniya suka tabbatar.

*Barkiya ɗan jarida ne mai zaman kan sa. Mai sharhi kan al’amurran tattalin arziki, tsaro da siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *