Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin ƙarfafa kasuwa da nufin farfaɗo da noma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin kayan abinci da ake gani a kasuwanni a ‘yan kwanakin nan, na da nasaba da manufofi da matakan musamman da aka dauka domin gyara harkar kasuwa da karfafa samar da abinci a cikin gida.

Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yayin taron majalisar noma ta kasa karo na 47 da aka gudanar a Kaduna, ranar Alhamis 6 ga Nuwamba, 2025.

A cewar ministan, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki alkawarin tabbatar da ikon cin gashin kai a fannin abinci, inda Najeriya za ta rika samar da abincin da take ci, tare da tabbatar da wadatar kayayyaki a farashi mai sauki.

Ya ce, “Mun riga mun fara ganin sakkowar farashin wasu muhimman kayan abinci a kasuwa, wanda hakan ke nuna tasirin matakan da gwamnati ta ke dauka. Ko da yake ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma wannan alamar tana tabbatar da cewa muna tafiya a madaidaiciyar hanya.”

Kyari ya bayyana cewa shirin National Agricultural Growth Scheme–Agro-Pocket (NAGS–AP), wanda ake aiwatarwa tare da hadin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) da jihohi, shi ne ginshikin inganta samar da kayayyakin noman da kuma bunkasa amfanin gona.

Ya ce yawan jahohin da ke noma alkama ya karu daga 15 a zangon damina na 2023/2024 zuwa karin jihohi a zangon 2024/2025. Haka kuma, a watan Oktoba da ya gabata, an kaddamar da noman Alkama na rani (rainfed wheat) a Kuru, Jihar Filato, wani sabon salo da Cibiyar Binciken Tafkin Chadi ta kirkiro domin ba da damar noman alkama ba tare da dogaro da ban ruwa ba.

Ministan ya kara da cewa, “Wannan sabuwar fasaha za ta bai wa Najeriya damar yin noman alkama a ko’ina cikin shekara, musamman a yankunan Filato, Taraba da Kuros Riba, wanda zai taimaka wajen cimma burin wadatar alkama a gida.”

Don rage asarar amfanin gona bayan girbi da daidaita farashin kayayyaki, gwamnati ta kaddamar da Nigeria Postharvest Systems Transformation Programme (NiPHaST) tare da Alliance for a Green Revolution in Africa (AGRA).

Kyari ya kuma bayyana cewa gwamnati ta amince da Naira tiriliyan 1.5 domin sake karfafa Bankin Noma (Bank of Agriculture), tare da karin Naira biliyan 250 da za a ware domin tallafawa kananan manoma.

Haka kuma, an kaddamar da shirin national mechanisation programme tare da hadin gwiwar Heifer Nigeria domin taimakawa matasa da mata su kafa cibiyoyin injinan noma a dukkan yankunan kasar.

A nasa bangaren, Karamin Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, ya bukaci a rungumi climate-smart agriculture, wato dabarun noma masu jituwa da yanayi domin dorewar samar da abinci.

Ya bayyana wasu muhimman shirye-shirye kamar shirin noman damina mai fadin hekta dubu 500, shirin samar da ruwa ta hasken rana, da kuma “Every Home a Garden” da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, domin karfafa noman gida.

A jawabinsa na bude taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce, “A wannan lokaci da muke ciki, batun samar da abinci ya wuce batun manufa kawai, ya koma batun rayuwa da dorewar kasa.”

Ya bayyana cewa karkashin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu, gwamnati ta sanya noma a matsayin jigon tattalin arzikin kasa, ta hanyar inganta sarkar samar da kayayyaki, da sabunta kayan more rayuwa a karkara.

Gwamnan ya ce, a Kaduna, gwamnati ta mayar da noma “ba wai sana’a kawai ba, amma ginshikin cigaba da tushe na walwala.”

Kafin bude taron, ministoci da jami’an ma’aikatar sun kai ziyarar gani da ido zuwa wasu cibiyoyin noma kamar De-Branch Farmers, Afrexim Bank Quality Assurance Centre, Olam Agri, Tomato Jos, da TMDK Agro Park, inda suka yaba da irin ci gaban da ake samu wajen kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi a karkara.

An kammala taron da bayar da lambar yabo ga manoma da ‘yan kasuwa da suka nuna bajinta a fannin noma da bunkasa abinci a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *