Rahoto Daga CBN
Ashafa Murnai Barkiya
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya nuna yabawa dangane da kyakkyawar shaida da jinjina tare da ɗaga matsayi da Cibiyar Bin-diddigin Tattalin Arziki ta Duniya, S&P Global Ratings ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya.
S&P Global Ratings dai a wani rahoton ta na baya-bayan nan, ta nuna gamsuwa da irin tsare-tsaren tsaftace hada-hadar kuɗaɗe da CBN ke yi, wanda cibiyar ta ce akwai yaƙini nan da ‘yan shekaru kaɗan masu zuwa tattalin arzikin Nijeriya zai cimma nagarta da inganci mai ɗorewa.
“A yanzu Babban Bankin Nijeriya na da kyakkyawar damar cimma muradin sa na ƙarfara tattalin arzikin Nijeriya nan da ‘yan shekaru kaɗan.” Haka rahoton na S&P Global Ratings ya nuna.
Cardoso ya ce tun daga farkon wannan shekara ta 2025, aka fara ganin haske mai nuni da cewa tsarin hada-hada domin saisaita bunƙasa tattalin arziki yana tafiya a kan hanya ɗoɗar.
Ya ce wannan kyakkyawar shaida da aka yi wa Nijeriya na ƙara nuni da cewa yanzu a duniya an gamsu cewa Nijeriya da gaske take yi, kuma an daina shakku ko tababar makomar tattalin arzikin ƙasar nan.
Wannan rahoto da S&P ta fitar, zai ƙara zaburar da ɗimbin masu sha’awar zuba jari kwararowa da jarin su a Nijeriya, cike fa yaƙinin cewa tattalin arzikin ƙasa ba shi da wata tangarɗa.
Idan ba a manta ba, a ƙarshen watan Oktoba ma CBN ya yi farin cikin cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su, sakamakon kashin-kajin da masu aikata ta’addanci da masu zambar kuɗaɗe suka shafa wa ƙasar.
Wannan jarida ta buga labarin, inda a lokacin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa cire sunan Nijeriya daga ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su a duniya cewa, hakan tabbaci ne da ke nuna duniya ta gamsu da tsare-tsaren tattalin arzikin da wannan gwamnati ta bijiro da su.
Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙon Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hakama Sidi Ali ta sa wa hannu kuma ta fitar a ranar Asabar, ta nuna cewa duniya ta gamsu da tsare-tsaren harkokin kuɗaɗe da kuma gagarimin yaƙi da almundahanaha da zambar kuɗaɗen da ake kan yi a Nijeriya.
CBN ya ci gaba da cewa an cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke sa-ido kan su, bayan kwamitin sa-ido ɗin ya gani tare da tabbatarwa irin “gagarimin ci gaban” da Nijeriya ta samu wajen yi wa tsare-tsaren kuɗaɗe ragama da linzamin daƙile zambar kuɗaɗe da kuma datse hanyoyin safarar kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.
FATF dai ƙaƙƙarfar hukumar sa-ido ce ta duniya wadda ke lura kan hada-hada da harƙallar kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya. Ta bayyana cire sunan Nijeriya a ranar Juma’a, tare da ƙasashen Afrika ta Kudu, Mozambique, Burkina Faso.
Hakama Ali ta ci gaba da cewa cire sunan Nijeriya ya nuna irin kyakkyawan tasirin da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da CBN, Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Lura da Hada-hadar Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) da kuma EFCC suka yi.
“Rawar da CBN ya taka wajen samun wannan nasara ta shafi tabbatar da sa-ido sosai, tsara ƙa’idoji, gindaya sharuɗɗa da gudanar da ayyuka ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen hada-hadar kuɗaɗe.”
Daga cikin tsare-tsaren da FATF tare da Kafofin Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe na Afrika ta Yamma su ka yi wa bin diddigi, akwai tsarin lambobin sirrin bibiyar Tsarin Musayar Kuɗaɗe, wadda aka ƙirƙiro domin rage harƙalla a hada-hadar musayar kuɗaɗe.
Cire Nijeriya daga ƙasashen da ake kaffa-kaffa da su ɗin zai ƙara cire shakku kan Nijeriya, tare da faɗaɗa hada-hadar cinikayya tsakanin ƙasar da ƙasashen waje, cibiyoyi da masu zuba jari. Haka bankuna za su samu ƙarin hulɗoɗi da masu son haɗin gwiwa daga waje.
An dai saka sunan Nijeriya cikin kasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffa da su a cikin 2021, bayan duniya ta nuna rashin amincewa dangane da yadda salon yaƙi da zambar kuɗaɗe ke gudana, musamman wajen matsalar yadda ake samun safarar muggan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.
