Sojojin Operation MESA na 3 Brigade, tare da goyon bayan rundunar sojan sama da ’yan sanda, sun ceci mutane bakwai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Yankamaye Cikin Gari na karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na 3 Brigade, Kaptin Babatunde Zubairu ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare ranar 29 ga Nuwamba 2025, lokacin da rundunar ta samu kiraye-kirayen gaggawa kan harin ’yan bindiga a yankin.
Sanarwar ta ce sojojin sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, suka kuma samu nasarar ceto wadanda aka sace.
Sojojin sun bi sawun ’yan bindigar zuwa hanyar Rimaye, inda suka bude musu wuta tare da ƙoƙarin dakile harin.
Sanarwar ta ce ’yan bindigar sun tsere zuwa yankin Kankia a jihar Katsina, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano inda suke.
Kwamandan 3 Brigade ya yaba da kwazon sojojin da yadda suka dauki mataki cikin gaggawa. Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka a ayyukan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
