Ashafa Murnai Barkiya
A wani sabon tsarin ƙara kare haƙƙin kwastomomi masu hulɗa da bankuna da kuma kare su daga ɗibga asara, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da wani sabon umarni da ke wajabta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su mayar wa waɗanda suka faɗa cikin zambar ‘Authorised Push Payment’ (APP) kuɗin su cikin awanni 48.
Wannan dai wani muhimmin mataki da ya ke nufin ƙara kare masu gudanar da harkokin kuɗi daga yawaitar zambar da ake yi masu ta hanyar kafofin hadahadar na zamani.
Wato zambar APP ita ce salon damfara da ake yi idan mutum ya tura kuɗi da kan sa zuwa asusun masu damfara bisa yaudarar sa ta hanyar yin sojan-gona, yaudara ko yin alƙawarin bogi.
Sai dai kuma shi wannan ba kamar zambar da ‘yan dandatsa ke wa mutum kutse cikin asusun ajiyar ba ce, ba tare da sanin mai shi ba.
Masu aikata zamba da damfara ta ‘APP’ na amfani da dabarun yaudarar jama’a ne domin samun amincewar su har su tura masu kuɗaɗe.
CBN ya bayar da wannan ne Umarni ne da aka bayar mai ɗauke da sa hannun Rita I. Sike, wadda ita ce Daraktar Sashen Tsare-tsare da Ƙa’idojin Hadahadar Kuɗi ta CBN, ta sanya wa hannu a ranar Talata.
Umarnin dai ya fayyace yadda bankuna da cibiyoyin kuɗi za su gudanar da bincike, warware matsaloli, da kuma mayar da kuɗaɗen ga mutanen da suka shiga cikin taskun zambar ‘APP’.
CBN ta ce za a mayar wa mutum kuɗin sa ne bayan an kammala bincike tare da tantancewa, kuma dole ne a yi hakan cikin sa’o’i 48.
Sanarwar ta ci gaba da jaddada cewa binciken da mayar da kuɗin tilas a gudanar da su cikin adalci, kan lokaci a bisa gaskiya.
Haka nan kuma dokokin sun fayyace yadda za a yi idan abin ya shafi cibiyoyi fiye da ɗaya. A irin wannan yanayi, bankin da aka fara tura kuɗin daga gare shi dole ne ya sanar da bankin da ya karɓa cikin mintuna 30 bayan samun ƙorafi. Sannan dukkan su za su yi bincike tare, su gano kura-kuran da suka faru, su tantance adadin asarar, sannan su amince kan mayar da kuɗi da matakan kariya.
Umarnin na ɗauke da cewa a irin waɗannan lokuta, dole ne a kammala mayar da kuɗin wanda aka zambata cikin kwanakin aiki 16 daga ranar da aka fara bayar da rahoton lamarin.
Wannan matakin CBN ya ɗauka na daga cikin yunkurin sa na ƙarfafa tsarin kuɗi da dawo da amincewar jama’a ga hanyoyin hadahadar kuɗi ta zamani a Najeriya.
A ƙarƙashin waɗannan ka’idoji, mutanen da abin ya shafa dole ne su bada rahoton zambar da aka yi masu ta ‘APP’ cikin awanni 24, ko kuma awanni 48 idan akwai buƙata.
Rahoton zai ƙunshi bayanan ma’amala, bayanan wanda aka tura wa kuɗi, da wasu takardun da ke nuna cewa tabbas an damfari mutum.
Da zarar an kai ƙorafi, to dole ne su kuma cibiyoyin kuɗi su tabbatar da karɓa cikin awanni 24, su ba da lambar shaidar karɓar ƙorafi, sannan su bayyana lokacin kammala bincike.
CBN ta kuma gargaɗi bankuna cewa rashin gudanar da bincike cikin lokaci ba tare da uzuri ba na iya zama karya dokar kare masu amfani da bankuna, wanda ka iya jawo hukuncin a kan bankunan kan su.
Sai dai kuma CBN ya ce duk wanda aka yi wa zamba, to kada ya yi jinkirin bayar da rahoto fiye da awanni 72, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran uziri ba, kamar rashin lafiya ko kuma sai daga bayan wasu kwanaki sannan ya gane ashe zamba ce aka yi masa.
