Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkinsu na dimokuraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar da safiyar Lahadi.
A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Binin ta aikawa Najeriya da buƙatu biyu na gaggawa, ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, tana neman a turo da jiragen yaƙin saman Najeriya domin kwace tasoshin da sojojin da suka yi juyin mulkin suka mamaye, ciki har da Talabijin na ƙasa da kuma wani sansanin soja.
Najeriya ta amsa wannan kira nan take, inda Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta NAF ta shiga sararin samaniyar Binin domin kawar da barazanar.
Haka kuma gwamnatin Binin ta roƙi a tura ƙarin jiragen leƙen asiri da kuma sojojin ƙasa na Najeriya, domin taimaka musu a ayyukan tsaro da kariyar manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin hukumomin tsaron Binin.
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan bukatun da ƙasar Binin ta nema, ciki har da zuwan sojojin Najeriya cikin ƙasar.
Yunƙurin juyin mulkin dai ya faru ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanar Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da muhimman hukumomin dimokuraɗiyya.
Sai dai da taimakon dakarun Najeriya, jami’an gwamnati masu biyayya ga Shugaba Talon sun kwace tashar Talabijin ɗin da sauran wuraren da aka mamaye, lamarin da ya kawo ƙarshen yunkurin juyin mulkin.
Da yake martani bayan tabbatar da dawowar tsarin dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya bisa rawar da suka taka.
“A yau, rundunar sojin Najeriya ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin mulki a Jamhuriyar Binin bisa gayyatar gwamnatin ƙasar. Sun yi aiki bisa ka’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki,” in ji Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Binin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
