An saki dukkan ɗaliban makaranta da aka sace daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja.
An kubutar da rukunin ƙarshe mai ɗalibai 130, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka ceto gaba ɗaya zuwa 230.
Jami’an Ofishin Mai baiwa sugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Ƙasa sun tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.
Wannan cigaba ya kawo ƙarshen kwanaki na damuwa da tashin hankali da iyalan waɗanda abin ya shafa suka shiga, da kuma nuni da gagarumar nasara ga hukumomin tsaro,da suka jagoranci aikin ceton.
An sace ɗaliban ne lokacin da ’yan bindiga suka kai hari makarantar kwanan, lamarin da ya haifar da ƙorafi a faɗin ƙasar tare da sake tayar da muhawara kan batun tsaron makarantu a Najeriya.
Hukumomi sun bayyana cewa sakin dukkan waɗanda aka sace ya biyo bayan matsin lambar jami’an tsaro ba kakkautawa da kuma haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, yayin da ake ƙara kira ga ƙarfafa tsaron makarantu da ɗaukar matakan da suka dace domin hana faruwar irin waɗannan hare-hare nan gaba.
