Daga yanzu, duk wata ƙungiya ko mutane masu ɗauke da makamai da ke sace mutane, kai hari ga manoma, ko ke tayar da hankalin al’umma a faɗin ƙasar nan an ayyana su a matsayin ’yan ta’adda. A yanzu lokacin kiran masu ta’addanci da sunaye daban daban ya riga ya wuce.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, yayi wannan bayanin ne a wajen taron manema labarai na karshen sherar 2025 a yau Litinin, a Abuja.
