Kowanne bangare na ƙasar nan zai amfana da yarjejeniyar kiwon lafiya da aka kulla tsakanin Najeriya da gwamnatin Amurka Cewar Ministan yaɗa labarai

Kowanne bangare na ƙasar nan zai amfana da yarjejeniyar kiwon lafiya da aka kulla tsakanin Najeriya da gwamnatin Amurka.
A cikin yarjejeniyar ta dala biliyan 5.18 da aka rattaɓawa hannu tsakanin ƙasashen biyu babu inda ke ɗauke da bayanin cewa mabiya addinin wani ɓamgare ne kaɗai zasu amfana da wannan tsarin karfafa kiyon lafiya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, yayi wannan ƙarin haske ne yayin taron manema labarai na karshen shekarar 2025 a jiya Litinin, a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *