Hukumar CAC ta zama ginshiƙin amintaccen tattalin arzikin Nijeriya, inji Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da gaskiya, aiwatar da sauye-sauye a hukumomi, da sauƙaƙe harkokin kasuwanci, inda ya bayyana cewa haɗin gwiwar hukumomi shi ne ginshiƙi wajen cimma manufofin Shirin Sabunta Fata Nagari na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin Shugaban Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC), Hussaini Ishaq Magaji, wanda ya jagoranci tawagar hukumar zuwa ziyarar ban-girma kafin bikin cika shekara 35 na hukumar mai taken CAC@35.

Yayin da yake yaba wa hukumar, Ministan ya ce CAC ta fuskanci sauye-sauye masu ban-sha’awa waɗanda suka sanya ta zama “babban jigo wajen kyautata yanayin kasuwanci da amincin tattalin arzikin Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da ke gudana a CAC, musamman ta fuskar amfani da fasaha, sun yi daidai da shirin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.

Idris ya yaba wa rawar da CAC take takawa wajen sauƙaƙe harkokin kasuwanci, ƙarfafa tsarin tafiyar da kamfanoni, da haɓaka amincewar masu zuba jari, yana mai jaddada cewa irin waɗannan sauye-sauyen suna da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa.

Haka kuma, ya yaba da gudunmawar hukumar wajen cire Nijeriya daga jerin FATF na ƙasashen da ake sanya wa ido, wanda ya ce babban mataki ne da ke nuna yadda duniya take ƙara amincewa da tsarin gaskiya na Nijeriya.

A cewar sa, ba za a faɗi nasarorin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ciki har da ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, rage hauhawar farashi, ƙaruwar amincewar masu zuba jari, da daidaituwar tattalin arziki, ba tare da an ambaci rawar da hukumomi masu rungumar sauye-sauye irin su CAC suke takawa ba.

Ministan ya ƙara da cewa CAC ta ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan ayyukan hukumar, domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun samu cikakken bayani game da sababbin abubuwa, ayyuka, da nasarorin hukumar.

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da tallafa wa CAC wajen yaɗa labaran sauye-sauye da shirye-shiryen ta.

Tun da farko, sai da Shugaban na CAC, wato Hussaini Ishaq Magaji, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin gayyatar ministan zuwa bikin cika shekara 35 na hukumar da kuma gabatar masa da rahoton nasarorin da aka samu a ƙarƙashin wannan shugabanci.

Manyan jami’an da suka halarci taron sun haɗa da Babban Sakataren Ma’aikatar, Mista Ogbodo Chinasa Nnam; Darakta a Taskar Bayanan Ƙasa, Dakta Evelyn Odigboh; Darakta a Sashen Hulɗa da Jama’a da Furotokol, Dakta Haruna Suleiman; da kuma Mataimaki na Musamman ga Minista kan Harkokin Gudanarwa, Dakta Sunday Baba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *