Limamin da ya jagoranci ɗaurin auren ’ya’yan Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Bello Matawalle, Farfesa Luqman Zakariyah, ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’a, yana mai cewa mulkinsa zai dawo da kyakkyawan fata a cikin al’umma.
Farfesa Zakariyah ya yi addu’ar ne a ranar Juma’a a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, yayin da Shugaba Tinubu ya halarci ɗaurin auren, inda ya wakilci yayan Matawalle a matsayin uba ga amarya da ango.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar São Tomé da Príncipe, Carlos Manuel Vila Nova, na daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron.
Limamin ya ce, “Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ba Shugaban Ƙasarmu, wanda ke wakiltar kowa, lafiya da tsawon rai, Ya kuma ba shi nasara da albarka a shugabancinsa. Muna addu’ar mulkinsa ya zama abin kyakkyawam fata ga yan ƙasa.”
Matawalle, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, ya aurar da ’ya’yansa mata guda biyar, Maryam, Safiyya, Farida, Nana Firdausi da Aisha, yayin da ’ya’yansa maza guda biyar, Ibrahim, Abdul Jalal, Surajo, Bello da Fahad, su ma suka yi aure.
Shugaba Tinubu ya yi waliycin amaryan a madadin iyalan Matawalle, inda limamin ya kuma yi addu’ar Allah Ya albarkaci auren, Ya ba ma’auratan zaman lafiya da nasara a rayuwarsu.
Gwamnonin jihohi, ’yan Majalisar Tarayya, mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya, manyan hafsoshin tsaro, ’yan diflomasiyya, sarakunan gargajiya, malamai da sauran al’umma duk sun halarci ɗaurin auren.
