Ashafa Murnai Barkiya
Bayanan da Babban Bankin Njeriya (CBN) ya fitar cikin wannan mako sun nuna cewa ma’aunin ƙarfin harkokin tattalin arzikin ƙasar sun ci gaba da nuna ƙarfi sosai a watan Janairu 2026, inda Ma’aunin hadahadar cinikayya a masana’antu, kamfanoni da kasuwanci, wato (Purchasing Managers’ Index – PMI) na CBN ya ƙaru zuwa maki 55.7.
Rahoton PMI da CBN ta fitar ya nuna cewa an samu faɗaɗa tattalin arziki na tsawon watanni goma sha huɗu a jere, tun daga watan Disamba na 2024 zuwa Janairu 2026.
PMI dai wata muhimmiyar alama ce ta gaba-gaba da ake amfani da ita wajen auna inganci da kuma tasirin ƙarfin masana’antu da kamfanoni masu zaman su, ta hanyar fannin samar da kayayyaki, sabbin oda, ɗaukar ma’aikata, lokutan isar da kayayyaki daga masu kaya, da adana kaya.
Awon maki ya haura maki 50, to hakan na nuna an samu faɗaɗar tattalin arziki. Yayin da idan an samu ƙasa da hakan ke nuna samun naƙasu, ko rashin yin hoɓɓasa.
Bayanan sun nuna ingantuwar yanayin kasuwanci a fannoni da dama tun farkon shekarar, inda aka samu faɗaɗa a yawancin manyan sassa da ƙananan sassa na tattalin arzikin Nijeriya, abin da ke ƙara tabbatar da alamun farfaɗowar tattalin arziki a hankali.
Bayanan PMI na watan Janairu ya ci gaba da kasancewa sama da ma’aunin maki 50 da ke raba yanayi na faɗaɗa da kuma hali na shiga tasku, lamarin da ke nuna ci gaba da ingantuwar samarwa, buƙata, da kwarin gwiwar ’yan kasuwa a sassan noma, masana’antu, da ayyuka.
Waɗannan sabbin bayanan PMI sun bayyana cewa an samu faɗaɗa tattalin arziki a kusan dukkan manyan sassan tattalin arzikin ƙasa a lokacin bitar su ɗaya bayan ɗaya. Daga cikin ƙananan sassa 36 da binciken CBN ya ƙarƙare, 31 sun nuna ci gaba, abin da ke nuna girman farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya.
PMI na gama-gari ya tsaya a maki 55.7 a watan Janairu 2026, wanda ke nuna wata na goma sha huɗu a jere na faɗaɗar tattalin arziki.
Sashen masana’antu ya samu ma’aunin PMI na maki 56.0, inda ƙananan sassa 14 daga cikin 17 suka nuna ƙaruwa a samarwa da sauran ayyuka masu alaƙa da juna.
Sashen ayyuka ya samu makin PMI 54.5, yana ƙara tsawaita jerin faɗaɗar sa zuwa watanni goma sha biyu a jere, inda ƙananan sassa 12 daga cikin 14 suka bayar da rahoton ci gaba.
Sashen noma ya samu PMI na maki 54.2, wanda ke nuna wata na goma sha takwas a jere na faɗaɗar tattalin arziki, inda dukkan ƙananan sassan noma biyar da aka bincika suka nuna ci gaba mai kyau.
Gaba ɗaya, rahoton bibiya da bin-diddigin PMI na nuna ɗorewar yanayin buƙata da kuma ingantuwar yanayin gudanar da aiki a matakai daban-daban na tattalin arzikin ƙasa, abin da ke ƙarfafa fata mai kyau game da aikin tattalin arziki a nan gaba kaɗan.
Bayanan yadda sassa suka yi daban-daban a binciken PMI na watan Janairu ya fa juriya da jajircewar su wajen bunƙasa.
Faɗaɗar da aka samu a sashen masana’antu na nuna ci gaba da ayyuka a masana’antu da sassan da ke da alaƙa da su, tare da tallafin tabbatacciyar buƙata da ingantuwar yanayin samarwa.
A sashen ayyuka kuwa, ci gaba da ake samu na nuna jajircewar kasuwanci, sufuri, da ayyukan ƙwararru, waɗanda suka ci gaba da zama muhimman alƙiblar da ke murɗa tattalin arziki.
Tsawaita faɗaɗar da aka samu a sashen noma na nuna ci gaba mai ɗorewa a fannin amfanin gona, sarrafa amfanin gona, abin da ke nuna ƙarin kwanciyar hankali a ƙoƙarin samar da abinci da bunƙasar tattalin arzikin yankunan karkara.
CBN ta bayyana cewa wannan faɗaɗa da aka samu a fannonin noma, masana’antu, da ayyuka na nuna ƙaruwa a ƙwarin gwiwar ’yan kasuwa, tare da tallafin daidaitaccen yanayin buƙata da kuma farfaɗowar sassan samarwa a hankali.
A cewar Babban Bankin, yadda ma’aunin PMI ya yi ya dace da babban burin sa na tabbatar da kwanciyar hankalin farashi tare da tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
A watan Disamba 2025, sashen kamfanoni da masana’antu masu zaman kan su a Nijeriya ya faɗaɗa da sauri fiye da kowane lokaci a shekarar, inda ma’aunin PMI na gama-gari ya tashi zuwa maki 57.6.
Wannan karatun na Disamba shi ne mafi ƙarfi a duk shekarar, yana nuna ƙaruwar ayyukan tattalin arziki a fannoni daban-daban tare da shimfiɗa kyakkyawan fata ga farkon shekarar 2026.
