Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin Arewa-ta-Tsakiya bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar kusan mutane 75 a Jihar Kwara.
Idris ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sa, sabon farmakin tsaron, wanda aka yi wa laƙabi da “Operation Savannah Shield,” ya haɗa da tura dakarun soji, jami’an ’yan sanda da jami’an rundunar tsaron daji na ƙasa domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa manufar matakin shi ne kare fararen hula a al’ummomin da ke fuskantar barazana bayan abin da ya bayyana a matsayin harin ta’addanci na matsorata da aka kai a Jihar Kwara.
Ministan ya ce rundunonin tsaron na samun tallafin fasahar tattara bayanan sirri da kuma tsarin ba-ta-kashi na gaggawa.
Ya bayyana cewa ana gudanar da wannan aiki ne a ƙarƙashin faɗaɗa hurumin tsaro da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa, lokacin da ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaron ƙasa a ranar 26 ga Nuwamba, 2026.
A cewar Idris, Shugaban Ƙasar ya yi Allah-wadai da hare-haren na Kwara, inda ya bayyana su a matsayin “na dabbanci, maras tausayi, kuma alamar wata fafutuka ta ’yan ta’adda da ta riga ta gaza, wadda ke kai hari kan fararen hula marasa kariya.”
Ya kuma ba da umurnin cewa “a yi amfani da dukkan ƙarfin gwamnati wajen hukunta duk masu kawo barazana ga zaman lafiya.”
Ministan ya ƙara da cewa tare da ƙara yawan jami’an tsaro a al’ummomin da ke cikin haɗari, Shugaban Ƙasa ya nuna ƙudirin gwamnatin sa na kare rayukan ’yan Nijeriya da kuma tabbatar da ’yancin su na yin addini cikin walwala.
Haka kuma, a cewar sa, an ƙarfafa tsaro a wuraren ibada, ciki har da ƙara yawan jami’an tsaro a kewayen majami’u a ranakun Lahadi, tare da haɗin gwiwa da shugabannin al’umma da na addini.
A wani ɓangare na ƙarfafa tsarin tsaro gaba ɗaya, Ministan ya ce Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta janye jami’an ta da ke raka manyan mutane zuwa ayyukan sintiri da tsaron al’umma a faɗin ƙasar nan.
Idris ya ce wannan matakin ya haifar da ƙarin tsaro a jihohin Kwara, Plateau, Binuwai, Kogi, Nasarawa, Neja, da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT).
Haka nan, ya ce Shugaba Tinubu ya sha jaddada cewa yaƙin da Nijeriya take yi da ta’addanci zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin jagorancin Nijeriya, ko da yake ana maraba da haɗin gwiwa daga abokan hulɗa na ƙasashen duniya idan buƙatar hakan ta taso.
Ya ce: “Yaƙin da Nijeriya take yi da ta’addanci zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin jagorancin Nijeriya kuma bisa ikon ta. Inda ya dace kuma ya yi daidai da muradun ƙasa, gwamnati tana maraba da haɗin gwiwa mai faɗi, ciki har da daga Amurka da sauran abokan hulɗa ta fannin tattara bayanan sirri da sa ido, domin tallafa wa manufofin da Nijeriya ta tsara, kuma domin amfanin ’yan Nijeriya.”
