An kubutar da Masu Ibada 38 da aka sace a wajen Ibada a Jihar Kwara da Ɗalibai 51 da aka sace a Jihar Neja — Gwamnatin Tarayya

Fadar Shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa an kubutar da dukkan mutane 38 da aka yi garkuwa da su a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, Jihar Kwara, yayin da wasu 51 cikin daliban makarantar Katolika da ke Jihar Neja suma aka gano su bayan sace da yan bindiga sukai a makon da ya shuɗe.

A cikin wata sanarwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya wallafa a shafin sa na X, ya ce ya dage tafiyar sa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu ne domin mayar da hankali kan batun tsaro, lamarin da ya ce ya fara haifar da sakamako.

Shugaba Tinubu ya ce yana karɓar rahotanni kai tsaye daga dakarun da ke fafatawa a fagen fama, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ba wajen tabbatar da tsaron kowane yanki na ƙasar.

Ya ce: “Kowane ɗan Najeriya na da haƙƙin zama lafiya a ko’ina cikin ƙasar. A ƙarƙashina, za mu tsare ƙasar, mu kuma kare mutanenmu.”

A halin yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da aikin dawo da sauran waɗanda ba a gano su ba, tare da tabbatarwa iyalai cewa kokarin kubutar da su na ci gaba da gudana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *