Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa an tsara kasafin kuɗin 2026 ne domin ƙarfafa nasarorin da tsarin shirye-shiryen Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka fara samarwa, waɗanda tuni suka fara nuna sakamako mai kyau.
Ministan ya bayyana hakan ne a wani sharhin sa da aka wallafa a jaridun ƙasar nan ranar Litinin, mai taken “Muhimmin Lokaci A Nijeriya: Hujjar Da Ta Sa Hanyar Da Aka Ɗauka Ita Ce Mai Ɓullewa.”
A sharhin, Idris ya ce: “’Kasafin Kuɗin Ƙarfafa Ƙasa, Sabuwar Juriya da Wadata ta Bai-Ɗaya’ yana da matuƙar muhimmanci.
“Alƙawari ne na ƙara himma kan abin da ke aiki, da ƙarfafa nasarori, tare da tabbatar da cewa cigaban bai-ɗaya da muke magana a kai ya zama abin da ‘yan Nijeriya da dama za su fara ji a rayuwar su ta yau da kullum.”
Ya bayyana cewa watanni 31 da suka gabata sun kasance lokaci na sauye-sauye masu wahala amma masu muhimmanci, inda aka ɗauki muhimman matakan tattalin arziki domin kawo ƙarshen durƙushewar da ta daɗe tana addabar ƙasa da kuma gina makoma mai ɗorewa.
Ministan ya ce alamun cigaba sun fara bayyana, inda harkokin kasuwanci suke bunƙasa, amincewar masu zuba jari take ƙaruwa, hauhawar farashi yake raguwa, tare da ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen waje.
“Waɗannan ba alƙaluma kawai ba ne. Su ne tubalan ingantaccen sauyi mai ɗorewa a rayuwar yau da kullum ta ‘yan Nijeriya,” inji shi.
Ya kuma jaddada muhimmancin amana da kyakkyawar sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma, tare da sake tabbatar da ƙudirin sa na sanar da ‘yan Nijeriya dukkan manufofin gwamnati, ƙalubale da kuma cigaban da ake samu.
Dangane da shirye-shiryen da ke da tasiri kai-tsaye ga rayuwar jama’a, ministan ya bayyana shirin rancen ɗalibai na NELFUND, shirin Shugaban Ƙasa na iskar gas ta CNG domin rage kuɗin sufuri, da shirye-shiryen matasa kamar LEEP, Jubilee Fellows Programme da shirin 3MTT.
Ya kuma ce ana ci gaba da ƙoƙarin magance ƙarancin abinci ta hanyar sake zuba jari a Bankin Manoma da samar da injinan zamani.
A ɓangaren ababen more rayuwa, Idris ya ambaci manyan ayyuka kamar Ginin Babbar Hanyar Gaɓar Teku, Hanyar Sokoto zuwa Badagiri, bututun iskar gas ta AKK, da sabbin ayyukan jirgin ƙasa da ake sa ran za su rage farashi da kuma ƙarfafa haɗin kai a faɗin ƙasa.
Game da tsaro, ministan ya ce gwamnati na ƙara ɗaukar jami’ai, inganta kayan aiki, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen waje.
Ya kawo misalin ceto ɗaliban da aka sace kwanan baya a jihohin Kebbi da Neja a matsayin shaida ta sabon ƙudiri da mayar da hankali kan batun tsaro.
Duk da haka, ya amince cewa ‘yan Nijeriya da dama suna fama da wahalhalu, amma ya tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin hanzarta kawo sauƙi ta hanyar ci gaba da aiwatar da gyare-gyare.
Ya yi kira ga jama’a da su ɗauki gina ƙasa a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyan kowa, su shiga cikin tattaunawa mai amfani, su kare kadarorin jama’a, tare da ƙin yarda da yaɗa labaran ƙarya.
Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa Tinubu bisa jagoranci mai natsuwa da jajircewar sa, inda ya ce hulɗar da aka yi kwanan nan da Amurka ta taimaka wajen ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da kuma yaƙi da ta’addanci.
Yayin da sabuwar shekara take kankama, Idris ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da mai da hankali kan gaba.
“Mun shimfiɗa sabon tubali. Yanzu kuma dole mu gina gidan tare,” inji shi.
A ƙarshe, Idris ya sake jaddada cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da kasancewa ƙofar ta a buɗe take, mai aiki tuƙuru tare da daidaito wajen bayyana manufofi da ayyukan gwamnati, tare da yi wa dukkan ‘yan Nijeriya fatan zaman lafiya da shekara mai albarka.
