Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na Ƙasa, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewa jihohin Arewa 19 sun samu raguwar bashin da ake bin su da kaso 42.06 cikin ɗari, daga Naira tiriliyan 1.98 zuwa tiriliyan 1.14. Ya ce hakan ya samu ne sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a ƙasa.
Bagudu ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga mahalarta taron kwanaki biyu na Tunawa da Sir Ahmadu Bello, wanda aka gudanar a Kaduna domin ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.
Ministan ya ƙara da cewa jimillar bashin da ake bin dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja ma ya ragu da kaso 33.4 cikin ɗari, daga Naira tiriliyan 5.8 zuwa tiriliyan 3.8. Ya ce wannan ci gaba na nuna ingancin manufofin ƙudurin “Renewed Hope” da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa kuɗaɗen cikin gida na jihohi da rage dogaro da bashi.
Bagudu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nuna gaskiya da adalci wajen rabon kuɗaɗe, da kuma haɗa kai da jihohi da ƙananan hukumomi.